Sabon Shugaban Ma’ikata Farfesa Ibrahim Agboola Gambari ne mutum na shida da ya hau kujerar tun bayan kirkiro mukamin a shekarar 1999 lokacin da Najeriya ta koma turbar dimokuradiyya bayan mulkin soji na tsawon lokaci.
Shugaban Ma’aikata a Ofishin Shugaban Kasa shi ne mai ba da shawara mafi girma ga shugaban kasa a Najeriya.
Shugaban kasa ne ke da ikon nada mai rike da mukamin, kuma nadin ba ya bukatar sahalewar Majalisar Dattawa.
Shugaban Ma’aikatan ne ke kula da dukkan al’amuran gudanarwa na Ofishin Shugaban Kasa, yake kuma tsara jadawalin ayyuka ya kuma tace sakonnin da ke isa ga shugaban kasa, da ma wasu ayyukan da shugaban ka iya ba shi.
- Buhari ya nada tsohon ministansa ya gaji Abba Kyari
- Sarkin Ilori ya yi wa Buhari godiyar nadin Gambari
Karfin fada a jin mai rike da mukamin dai ya dogara ne a kan yadda shugaban kasar ya yarda da shi ya ke kuma amincewa da shawarwarinsa.
Ga sunayen wadanda suka rike mukamin zuwa yanzu:
1. Abdullahi Mohammed – Mayu 1999 zuwa Yuni 2008
Janar Abdullahi Mohammed mai ritaya ne Shugaban Ma’aikata a Ofishin Shugaban Kasa na farko.
Ya rike mukamin ne a zamanin mulkin farar hula na Cif Olusegun Obasanjo, sannan ya shiga shekara ta farko ta mulkin marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar’Adua.
Kafin nadinsa a wannan matsayin dai shi ne Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara a kan Al’amuran tsaro a zamanin mulkin soji na Janar Abdulsalam Abubakar.
Masharhanta sun ce Shugaba Obasanjo ya nada tsohon janar din a mukamin ne don cimma wasu muradu na bangarorin da suka hada hannu suka tabbatar ya hau kujerar shugaban kasa, yayin da ya yi tazarce a mulkin ’Yar’Adua don samar da wata madogara ga sabuwar gwamnatin kafin ta tsaya da kafafunta.
A ranar 2 ga watan Yunin 2008 ya yi murabus daga mukamin na Shugaban Ma’aikata a Ofishin Shugaban Kasa.
2. Gbolade Osinowo – Yuni 2008 zuwa Satumba 2008
Kafin nadinsa a matsayin Shugaban Ma’aikata a Ofishin Shugaban Kasa, Dokta Gbolade Osinowo mataimaki ne ga mai rike da mukamin kafin shi, Janar Abdullahi Mohammed.
Shugaba ’Yar’Adua ne ya nada shi ya maye gurbin Mohammed lokacin da janar din ya ajiye aikin.
Kafin nan ya taba zama babban mai ba da shawara a kan al’amuran siyasa ga Shugaba Olusegun Obasanjo, kuma an ce yana cikin mutanen da suka fi kusanci da tsohon shugaban kasar.
Ya yi aiki a matsayin Shugaban Ma’aikata har zuwa ranar 18 ga watan Satumba 2008 lokacin da Shugaba ’Yar’dua ya soke mukamin.
3. Mike Oghiadomhe – Mayu 2010 zuwa Fabrairu 2014
Daga ranar 18 ga watan Satumba na shekarar 2008 babu wanda ya rike mukamin Shugaban Ma’ikata har tsawon kusan shekara biyu.
Amma a ranar 17 ga watan Mayu 2010 Shugaba Goodluck Jonathan ya dawo da mukamin, ya kuma nada Mista Mike Oghiadomhe.
Shi dai Mista Oghiadomhe ya taba rike mukamin Mataimakin Gwamna a jihar Edo daga 1999 zuwa 2007.
Kafin nan kuma ya taba wakiltar al’ummar mazabarsa a Majalisar Wakilai ta Tarayya.
Ya rike mukamin Shugaban Ma’aikata ne dai har zuwa ranar 10 ga watan Fabrairun 2014 lokacin da ya ajiye aikin a wani yanayi mai cike da cece-ku-ce.
4. Jones Arogbofa – Fabrairu 2014 zuwa Mayu 2015
Bayan da Mike Oghiadomhe ya ajiye aiki, Shugaba Goodluck Jonathan ya maye gurbinsa da Jones Arogbofa.
Shi ma Arogbofa, kamar Abdullahi Mohammed, tsohon soja ne – lokacin da Shugaba Olusegun Obasanjo ya yi wa sojojin da suka taba rike mukaman siyasa a 1999 abin ya rutsa da shi yana matsayin Birgediya Janar.
Mista Arogbofa ya ce daya daga cikin abubuwan da ke ba shi takaici shi ne bai kai matsayin Manjo Janar ba kuma bai zama kwamandan bangaren sadarwa na rundunar sojin kasa ta Najeriya ba.
5. Abba Kyari – Agusta 2015 zuwa Afrilu 2020
A ranar 27 ga watan Agustan 2015 Shugaba Muhammadu Buhari, wanda aka rantsar ranar 29 ga watan Mayun shekarar, ya sanar da nadin Malam Abba Kyari a matsayin Shugaban Ma’aikata.
Tun daga lokacin har zuwa rasuwarsa a ranar 17 ga watan Afrilu, Malam Abba Kyari ya taka muhimmiyar rawa a al’amuran mulkin Najeriya.
Manazarta da dama sun yi amanna cewa babu wani mai rike da mukamin da ya samu karfin fada a ji kamar shi.
Lokacin da Shugaba Buhari ya shaida wa ministocinsa cewa duk mai so ya gana da shi ya biyo ta hannun Malam Abba kyari, an yi ta maganganu da dama, inda har wasu ke zargin marigayin da yin babakere a kan harkar mulki.
Sai dai kuma ya sha yabo bayan rasuwarsa har a wajen masu suka saboda yadda ya rike amanar shugaban kasar, ya kuma zama kariya ga maigidan nasa a tsawon lokacin da ya yi yana rike da mukamin.
6. Farfesa Ibrahim Agboola Gambari
Abin tambaya dai shi ne, ko sabon Shugaban Ma’aikata Ibrahim Gambari zai taka rawa irin wadda marigayi Abba Kyari ya taka?
Ban da wannan kuma, kasancewar yana cikin mutanen da ke kusa da Shugaba Buhari lokacin yana mulkin soji, ko zai fada a ji kamar Abba Kyari?