✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban kwamitin tsaro ya shawarci ’yan Arewa

  Shugaban kwamitin zaman lafiya hadin kai, tsaro da kuma ci gaba na Kurosriba, Alhaji Ya’u Isma’il Girei ya bayyana cewa ’yan Arewa mazauna Kurosriba…

 

Shugaban kwamitin zaman lafiya hadin kai, tsaro da kuma ci gaba na Kurosriba, Alhaji Ya’u Isma’il Girei ya bayyana cewa ’yan Arewa mazauna Kurosriba suka daure suka ci gaba da bayar da hadin kai domin a gudu tare a kuma tsira tare, ba ma al’ummar yanzu mazauna jihar ne kadai za su ci gaba cin amfanin kwamitin ba, har ma wadanda za su zo nan gaba.

Shugaban ya fadi haka ne, a lokacin da al’ummar Arewa mazauna Kurosriba suka kai masa ziyara a ofishinsa, kwanakin baya. Kwamitin na tsaro da samar da zaman lafiya, an kafa shi ne a watannin baya da nufin samar da zaman lafiya tsakanin ’yan Arewa da kuma sauran kabilu mazauna Kurosriba, kana kuma da wanzar da tsaro saboda bata-gari kada su rika shigowa unguwar Hausawa da ke Layin Bagobiri suna aikata miyagun laifuka suna tserewa, kamar yadda a can baya wasu ’yan fashi suka rika bin wasu ’yan Arewa a unguwar suna yi masu fashi.

“Idan da za mu daure, za mu ci amfanin wannan kungiya, ba don komai ba sai don kara samun zama lafiya. Kana kuma ba mu a yanzu ba, hatta ’ya’ya da jikoki da ma wadanda Allah zai kawo zama Kurosriba, duk za su ci gaba da morewa da wannan kyakkyawan fandisho da aka kafa,” inji shugban. Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba za su karade sauran manyan garuruwan jihar domin jawo ’yan Arewa zuwa cikin kungiyar. Ya ce nan kusa, kwamitinsa zai kara samun tagomashi musamman ma yanzu da suka samu yarda da kuma amincewar gwamnatin jiha.