✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Kasar Tunisiya ya rasu

Fadar Shugaban Kasar Tunisiya ta sanar da rasuwar Shugaba Beji Caid Essebsi, wanda ya rasu yana da shekara 92. Beji shi ne Shugaban Kasar da…

Fadar Shugaban Kasar Tunisiya ta sanar da rasuwar Shugaba Beji Caid Essebsi, wanda ya rasu yana da shekara 92.

Beji shi ne Shugaban Kasar da ya fi kowa tsufa a duniya. An kwantar da shi a asibiti ranar Laraba amma ba a fadi dalilin rashin lafiyarsa ba. A shekerar 2014 ne Mista Essebsi ya lashe zaben farko bayan boren kasashen Larabawa.

Mista Essebsi ya kuma kwanta a asibiti a watan da jiya bayan fama da abin da jami’ai suka kira “rashin lafiya mai tsanani.”

Ba su yi karin bayani kan batun ba. Firayi Minista Youssef Chahed, wanda ya ziyarce shi a asibiti, ya roki mutane su daina yada “labaran karya” a kan halin da Shugaban ke ciki.

A kundin tsarin mulkin kasar, Mista Chahed zai iya zama Shugaban Kasa na tsawon kwanakin da ba za su wuce 60 ba ko kuma zuwa lokacin da za a zabi sabon Shugaba. A farkon bana ne ya sanar da cewa ba zai tsaya a zaben da za a sake yi a watan Nuwamba ba. A wani taro da ya shaida wa jam’iyyarsa ta Nidaa Tounes cewa ya kamata wani mai jini a jika ya karbi ragama. Ya ce lokaci ya yi da “za a bai wa matasa dama.”

Mista Essebsi tsohon lauya ne da ya yi karatu a birnin Paris na Faransa.

A lokacin da yake dan siyasa na tsawon lokaci ya kuma yi Ministan Harkokin Cikin Gida da kuma Shugaban Majalisar Wakilai.

A shekarar 2011 ne aka hambarar da tsohon Shugaban Tunisiya Zine el-Abedine Ben              Ali bayan shafe shekara 23 a kan mulki kamar yadda BBC ya ruwaito. Tun sannan ake jinjina wa Tunisiya kasancewarta kasar da ita kadai ta hau turbar dimokuradiyya bayan boren kasashen Larabawa.

Sai dai a shekarun baya-bayan nan kasar ta sha fama da hare-haren masu ikirarin jihadi da tabarbarewar tattalin arziki, inda yawan marasa aikin yi ke ta’azzara.