Shugaban Kasar Sri Lanka, Gotabaya Rajapaksa, ya fice daga kasar sa’o’i kadan kafin cikar wa’adin sanar da murabus dinsa daga kujerarsa.
Ana zargin ya tsere daga kasar kafin sauka daga mukamin nasa ne don guje wa yiwuwar tsare shi bayan karewar wa’adin rigar kariyarsa idan ya yi murabus a cikin Sri Lanka.
- ‘Adadin fararen hular da aka kashe a rikicin Ukraine ya haura 5,000’
- DAGA LARABA: Yadda Matsalar Tsaro Da Rashin Tsari Suka Ruguza Ilimi a Zamfara
Masu zanga-zanga kan karancin man fetur da tsadar rayuwa a kasar ne dai suka tilasta wa gwamantin Shugaban Gotabaya Rajapaksa yin murabus, bayan sun mamaye Fadar Shugaban Kasa a ranar Asabar da ta gabata.
Boren da ya ci kujerar Shugaban Rajapaksa ya samo asali ne daga zanga-zangar da aka shafe watanni ana yi kan gazawar gwamnatin shugaban wajen shawo kan matsalar tabarbarewar tattalin arziki na tsawon shekaru a Sri Lanka.
Hukumomin kasar sun sanar cewa a safiyar Laraba Mista Rajapaksa da matarsa suka bar kasar zuwa Male, babban birnin kasar Maldives a cikin wani jirgin soji, da rakiyar dogaransa biyu.
A ranar Laraba Mista Rajapaksa zai sanar da saukarsa da kujerarsa ta shugaban kasa a hukumance, bayan ’yan kasar sun fatattake shi tare da Fira Ministan kasar daga gidan gwamnati.
Mamayar fustattun masu zanga-zangar a fadar gwamnati ta sa shugaban buya tare da amincewa ya sauka daga mukaminsa.
A halin yanzu, majalisar dokokin kasar ta yi ittifakin duk mambobinta za su yi murabus daga mukamansu domin ba da damar kafa gwamnatin hadin gwiwa da za kunshi duk bangarorin kasar.
Zuwa ranar Laraba da Gotabaya zai yi murabus ake sa ran majalisar za ta sanar da sabon shugaban kasar.