Shugaban kasar Kyrgyzstan, Sooranbi Jeenbekov ya sauka daga kujerarsa bayan kwana 10 ana rikicin siyasa a kasar.
A ranar Alhamis shugaban ya sanar da saukara domin kawar da fada tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar neman ya sauka daga mukaminsa.
- Kotu ta yanke wa Donald Trump da Sarki Salman hukuncin kisa
- Rikicin Azerbaijan da Armenia na iya shafar yanki –Iran
Tun ranar 4 ga watan Oktoba Kyrgiztan ta fada cikin rikici bayan ’yan adawa sun yi fatali da sakamakon zaben da ya nuna abokan Jeenbekov ne suka lashe zaben Majalisar Dokokin kasar.
Daga shugaban ya soke zaben bayan’yan adawa masu zanga-zangar sun kwace gine-ginen gwamnati.
Ya kuma sanar a makon jiya cewa zai yi murabus amma ya jinkirta da cewa sai an yi wani zabe.
A ranar Laraba, Jeenbekov ya amince da zabin majalisar na Sadyr Japarov, don ya zama firai minista.