✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Kasa ya yaba wa sojan sama da ya mayar da Naira miliyan 15 da ya tsinta

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa wani sojan sama mai suna ACM Bashir Umar kan mayar da Fam dubu 37 (kimanin Naira miliyan 15)…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa wani sojan sama mai suna ACM Bashir Umar kan mayar da Fam dubu 37 (kimanin Naira miliyan 15) da ya tsinta ga mai  kudin.

Wata sanarwa da ta fito daga Kakakin Shugaban Kasar Femi Adesina ta ce Shugaba Buhari ya bukaci ’yan Najeriya su yi koyi da sojan saman, inda ya ce, wannan kyakkyawan hali da ya nuna ya nuna cewa akwai kyakkyawar fata ga kasar na.

Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Sama, Iya Kwamanda Ibikunle Daramola ya bayyana cewa sojan saman ya tsinci kudin ne a Sansanin Alhazai na Jihar Kano lokacin da yake aiki tare da wadansu. “An yi sa’a  ya ga lambar waya a cikin jakar kudin don haka shi ma’aikacin namu ya kira mai kudin tare da damka masa kudinsa,” inji Daramola.

Rundunar Sojin Sama karkashin jagorancin Iya Mashal Sadikue Abubakar ta umarci Shugaban Sashen Gudanarwa na Rundunar Iya Bayis Mashal Kinsgley Lar ya yi abin da ya dace wajen saka wa Bashir Umar don karkafafa gwiwar sauran ma’aikatan rundunar ta yadda za su kasance masu dabi’u na kwarai da za su kara daga martabar rundunar a wajen al’ummar kasar nan.

Wannan ba shi ne karo na farko da sojan sama ke mayar da kayayyakin da aka mance a filayen jiragen saman kasar nan ba, domin a watan Agustan bara  ma an samu irin wannan kamar yadda BBC ya ce.