✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban karamar hukuma ya yi wa mai neman kujerarsa dukan kawo-wuka

A wurin taron sulhu aka lakada wa mai neman takarar duka aka sumar da shi.

Ana zargi Shugaban Karamar Hukumar Gaya a Jihar Kano, Ahmad Abdullahi Tashi da Shugaban Majalisar Kansilolinsa, Shu’aibu Gamarya da lakada wa wani mai zawarcin kujerarsa, Hafizu Sunusi Mahmoud Gaya dukan kawo wuka.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan siyasa masu neman tsayawa takara a matakin kananan hukumomi ke ta fadi tashin ganin sun kai bantensu gabanin zaben da za a yi a watan Janairun 2021.

Wani ganau kuma dan uwan dan takarar, Uwaisu Sunusi Mahmoud Gaya ya ce “suna ta dukan sa har suka sumar da shi ya daina magana bayan Ahmad Tashi ya bude wa kannensa biyu kofa sun shigo suka ci gaba da dukan Hafiz”.

Ya tabbatar wa Aminiya cewa lamarin ya auku ne misalin karfe biyu na ranar Laraba, a gaban kwamitin sasanta tsakanin ’yan takara da gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya kafa.

Hon. Hafizu Sunusi Mahmoud Gaya lokacin da ya yankin takardar tsayawa takarar shugabancin karamar hukumar Gaya a Jihar Kano.

An dai kafa kwamitin ne da nufin samar da sulhu tsakanin ’yan takarar gabanin shiga zaben fid da gwanin da za a yi a jihar.

Uwaisu ya ce, “Shugaban karamar hukumar ya bayar da umarnin duk wanda suka zo rakiyar dan takara su ba su sarari za su shiga sulhu, sai ya tashi tsaye shi da Gamarya suka kai wa wani mai neman takarar shugabancin Gayan kuma dan yayan Sanata Gaya Kamal Ibrahim Gaya duka.

“Daga bisani suka koma dukan Hafizu, suna ta dukan sa har suka sumar da shi ya daina magana…Da kyar muka ceci dan uwana Hafizu Sunusi daga hannunsu muka kai shi Asibitin Gaya.

“Daga baya sai Sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Gaya ya ba wa daya dan takarar, Kamal Gaya umarnin mu dawo da shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano don samun kulawa sosai saboda ko magana ba ya iya yi a lokacin, har suma ya yi”, inji Uwaisu.

Mun yi ta kokarin neman shugaban karamar hukumar Hon. Ahmad Tashi, don jin ta bakinsa amma wayarsa a kashe har zuwa lokacin da muke kammala wannan rahoton; mun tura masa sako ta waya, nan ma babu amsa.

‘Akwai tsamin dangantakar Siyasa’

Gaya, karamar hukuma ce da ke da rigingimun siyasa tsakanin jagorori da mabiya.

Ana zargin dukan Hafizun ba zai rasa nasaba ba da rashin jituwar da ke tsakanin tsagin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji da tsagin dan Majalisar Tarayya mai wakilatr mazabar Gaya da Ajingi da Albasu, Abdullahi Mahmud Gaya.

Dan takarar shugabancin karamar hukumar da ya tsallake rijiya da baya dai dan yayan dan Abdullahi Mahmud Gaya ne, amma a siyasance yana biyayya ne ga tsagin Sakataren Gwamnatin Jihar da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano Abdulaziz Gafasa.

Shi kuwa Shugaban Karamar hukumar da shi da shugaban kansilolinsa suna bangaren dan majalisa, Abdullahi Mahmud Gaya ne.

Wani makusancin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Ibrahim Alkali, ya tabbatar wa Aminiya da faruwar lamarin, da cewa tun ranar Alhamis Usman Alhaji ya nemi Sanata gaya da Abdullahi Mahmud kan lamarin, ya kuma yi Allah wadai da abun da ya faru.

%d bloggers like this: