Shugaban Karamar Hukumar Toto da ke Jihar Nasarawa, Prince Nuhu Dauda ya nada mutum 16 a matsayin mataimaka na musamman kan al’amuran karamar hukumar.
Hakan na kunshe cikin takardar nade-naden mukaman mai dauke da sa hannun zababben shugaban karamar hukumar da aka raba wa manema labarai a ranar Alhamis a garin Toto.
- Masarautar Zazzau: Lauyan Iyan Zazzau ya janye kara
- Jahilai ne ke juya al’amuran siyasa da gwamnati a Kano — Hadimin Ganduje
Shugaban karamar hukumar ya ce, an zabo hadiman ne da aka bai wa mukaman bisa cancantarsu da irin gudunmawar da suka bayar wurin ci gaban majalisar karamar hukumar.
Takardar nadin mukaman na dauke da sunayen da suka hada: Abdullahi Usman, Ahmed Alhaji, Umar Zakari, Mahmud Muhammed, Galadima Ibrahim Salihu, Jibrin Dikko, Khadijat Muhammed, Muhammed Ahmed, Isah Labaran da kuma Yusuf Ibrahim.
Sauran hadiman da aka nada a mukaman mataimaka na musanman sun hada da: Shuaibu Ahmed, Ayaga Gata, Usman Alhaji, Muhammed Baba da Iliyasu Bature.
Shugaban Majalisar ya ayyana sunan Iliyasu Alfa a matsayin mataimakin akawun shugaban majalisar Kansilolin karamar hukumar.
Sanarwa ta ce, dukkan hadiman da aka nada za su fara aiki nan take kamar yadda Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) ya wallafa.
Shugaban karamar hukumar ya tabbatar wa Jama’ar da ke yankin cewa, shugabancin karamar hukumar zai yi aiki da kowa don bai wa jama’a damar bayar da ta su gudunmawar da zata ciyar da karamar hukumar gaba dama Jihar baki-daya.