Shugaban Karamar Hukumar Eti-Osa da ke Jihar Legas, Hon. Olufunmi Rafiu Olatunji ya rasu.
Olufunmi, wanda tuni ya sake lashe zaben shugabancin Karamar Hukumar a karo na biyu a karkashin jam’iyyar APC ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya.
- Akwai yuwuwar na koma hada takalma ko koyarwa a 2023 – Gwamnan Abiya
- Yawancin ’yan bindigar da ke addabar mu ba ’yan Najeriya ba ne – Gwamnan Neja
Tuni dai aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
A zaben fid da gwanin APC na zaben Karamar Hukumar ranar 29 ga watan Mayu, marigayin ya sami kuri’u 1,977 inda ya lashe zaben tare da zama dan takara a zaben na 24 ga watan Yuli mai zuwa.
Babban limamin Masallacin Oloro da ke Ajah, Jamiu Moridiu ya shaida wa wakilinmu cewa mutuwar shugaban ba karamin rashi ba ce, saboda ya taka rawar gani yayin mulkinsa.
“Aikin Gwamnati yana da yawa kuma babu wanda zai iya kammala shi. Olufunmi ya yi iya kokarinsa, kuma za a jima ana tunawa da shi a kan haka,” inji shi.
Shi ma wani dan siyasa a yankin, Michael Collins ya ce mutanen yankin sun kadu da rasuwar matuka, yana mai cewa rasuwar za kuma ta haifar da babban gibi ga jam’iyyar APC da ma iyalan mamacin.
“Ina addu’ar Allah ya ba iyalansa da ma sauran makusantansa hakurin jure wannan babban rashin,” inji Michael.