✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban kamarar hukuma ya kaddamar da ayyukan N1bn a Kano

Shugaban Karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano ya kaddamar da aikin mayar da titi mai hannu biyu

Shugaban Karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano, Injiniya Abdullahi Garba Ramat, ya kaddamar da ayyukan sama da Naira biliyan daya a karamar hukumar.

Ayyukan da ya kaddamar sun hada da aikin mayar da titin da ya tashi daga Kwanar Ungoggo zuwa cikin garin Ungogo, ya zuwa mai hannu biyu, tare da yin kwalbatoci da magudanan ruwa a kowane bangare na titin mai tsawon kilomita biyar.

Sauran ayyyukan sun hdada da na gyaran Makarantar Firamaren Abdullahi bin Mas’ud da ke unguwar Bachirawa da kuma katange babbar Mahautar Bachirawa.

Kazalika shugaban karamar hukumar ta Ungogo ya kaddamar da aikin Masallacin Juma’a da Sallar Idi a Mazabar Karo da ke karamar hukumar.

Injiniya Ramat ya ce shugabancinsa a Karamar Hukumar Ungogo ya yanke shawarar gudanar da ayyukan ne bayan binciken da ta gudanar domin gano muhimman ayyukan da al’ummar karamar hukumar suke bukata.