Shugaban Kasar Chile Sebastian Piñera ya kori dukkan ministocin gwamnatinsa domin kafa sabuwar Majalisar Zartarwa tare da aiwatar da wasu gyare-gyare kamar yadda masu zanga-zanga a kasar suka bukata.
Zangar-zangar ta samo asali ne daga karin kudin shiga jirgin kasa da gwamnatin kasar ta yi, wanda tuni ta soke karin, amma duk da haka sai zanga-zangar ta rikide zuwa bukatar neman gyara game da tsadar rayuwa da kuma rashin daidaito a tsakanin ’yan kasar.
Har yanzu dai ba a san wane irin tsari zai bi ba wajen kafa sabuwar Majalisar Zartarwar tasa ba.
Sama da mutum miliyan daya ne suka hau tituna domin yin zanga-zangar lumana tare da kiran a kawo gyara game da yadda gwamnati ke amfanar ’yan kasar a babban birnin kasar Santiago.
Mista Piñera ya ce ya samu labarin bukatun nasu ne a gari.
Shugaban kuma ya bayyana cewa dokar ta-bacin da aka saka a wasu birane an dage ta.
’Yan adawa a kasar da ma sun yi ta kiraye-kirayen a janye dokar ta-bacin.
An samu sace-sace da fasa shaguna, yayin zanga-zangar, inda sama da mutum 7,000 aka kama.