✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Ajentina ga Messi: Kada ka yi murabus

kasa Ajentina, Mista Mauricio Macri ya buga wa Zakaran kwallon kafa na Duniya Lionel Messi waya yana rokon dan wasan na Barcelona da kada ya…

kasa Ajentina, Mista Mauricio Macri ya buga wa Zakaran kwallon kafa na Duniya Lionel Messi waya yana rokon dan wasan na Barcelona da kada ya bar buga wa kungiyar kwallon kafa ta kasarsa wasa.
Messi ya bayyana cewa zai daina buga wa kasarsa wasa a gasar kasashen duniya bayan da kasar Chile ta lashe Ajentina a wasan karshe na cin Kofin Nahiyar Amurka a ranar Lahadin da ta gabata, inda Messi ya gaza cin bugun finareti kuma ya fashe da kuka bayan an hura tashi.
Messi, wanda ya samu nasarar cin kofuna da dama a kungiyar kwallon kafa ta Bacelona da ke kasar Spain, har yanzu bai samu nasarar cin kofi ko daya ba da babban kungiyar kwallon kafa ta kasarsa Ajentina ba.
Messi ya fada wa manema labarai cewa: “Wasan kasa da kasa ya kare gare ni. Wannan shi ne karo na hudu da nake rashin sa’a a bugun karshe da kasar Ajentina, ba rabona ba ne. Ina ganin na riga na yanke shawara.
Messi mai shekara 29 a duniya ya ce: “A cikin dakin hutawar ’yan wasa ina jin wannan ne karo na karshe da zan buga wa kasata wasan kasa da kasa.”
Messi ya kara da cewa:
“Wannan shi ne abin da nake ji yanzu, ina cike da bakin ciki, a ce na sake zubar da finareti mai matukar muhimmanci.”
Sai dai Kakakin Shugaban Ajentina, ya shaida wa kafar Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa: “Shi (Shugaban kasa Macri) ya kira shi a waya, ya bayyana masa yadda yake alfahari da shi kan rawar da ya taka a babbar kungiyar kwallon kafa ta kasar, kuma ya bukaci ya toshe kunnuwansa daga masu suka.”
Shugaba Marci ya kuma tura sakon goyon bayansa ga Messi a shafinsa na Twitter.
A wasan na ranar Lahadi, an tashi babu ci a tsakanin Ajentina da Chile, inda kasar Chile ta samu nasarar lashe kofin a bugun finareti, kuma Messi ya barar da bugunsa.
Wannan ne karo na biyu da kasar Chile ta lallasa Ajantina a wasan karshe na gasar Kofin Copa America kuma duka a bugun finareti. Ajentina ta sha kashi a hannun kasar Jamus a gasan cin Kofin Duniya a shekaran 2014, kuma sun sha kashi a hannun kasar Brazil a shekarar 2007.