Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa dangane da rasuwar Darakta Janar na Cibiyar Horas da Manyan Jami’an Gwamnati a kan dabarun Shugabanci da Tsarin Gudanar da Jama’a (NIPSS), Farfesa Habu Galadima.
A wata sanar da Shugaban Kasar ya fitar ranar Lahadi ta bakin Mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, ya bayyana mamacin a matsayin wani jan gwarzo da ya tsaya tsayin-daka wajen inganta dabarun koyar da tsari na shugabanci.
- Mahara sun sace mai gari, sun kone gidaje a Neja
- Jami’an tsaro sun ba da belin Ali Baba bayan kalamansa a kan Kwankwaso
Yayin da mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da kuma gwamna da al’ummar jihar Nasarawa baki daya, Shugaba Buhari ya ce za a dade ana tunawa da marigayin saboda rawar da ya taka a fagen bunkasa harkokin ilimantarwa wanda kuma ya kware a gudanar da harkokin jama’a.
Shugaban Kasar ya ce rasuwar Farfesa Galadima za ta ci gaba da kasancewa babban rashi ga Cibiyar NIPSS da kuma Najeriya baki daya.
Ya yi addu’ar Allah ya yafewa marigayin kurakuransa tare da neman Ya yi masa sakayya da mafi kyawun makoma ta gidan Al-Janna.
Marigayi Habu Galadima ya yi gamo da ajali a safiyar yau ta Lahadi yana da shekaru 57 bayan ya yi fama da rashin lafiya takaitacciya.