Shugaba Muhammadu Buhari ya ce za a sassauta dokar hana fita da aka ayyana a jihohin Legas da Ogun da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya sannu a hankali.
A maimakon dokar hana fita gaba daya, a cewar shugaban kasar, za a kafa wata dokar ta hana fita daga karfe 8 na yamma zuwa karfe 6 na safe, kama daga ranar Litinin mai zuwa.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi da ya yi wa ‘yan Najeriya da maraicen Litinin.
“Bisa la’akari da…shawarwarin Kwamitin Cika-Aiki na Shugaban Kasa a Kan COVID-19, da kwamitocin gwamnatin tarayya daban-daban wadanda suka yi nazari a kan al’amuran da suka shafi tattalin arziki da zamantakewa, da kuma Kungiyar Gwamnoni ta Najeriya, na amince da sassauta dokar hana fita sannu a hankali a Yankin Babban Birnin Tarayya da jihohin Legas da Ogun kama daga ranar Litinin 4 ga watan Mayun 2020.
- Dokar zaman gida: Gwamnoni sun bukaci a bari a yi walwala
- Dokar hana fita: Kwalliya na biyan kudin sabulu?
“Sai dai kuma za a biyo bayan wannan da kara zage dantse wajen yin gwaji da bibiyar wadanda suka yi mu’amala da wadanda aka tabbatar sun kamu yayin da ake maido da wasu harkokin kasuwanci da tattalin arziki a wasu bangarori”, inji Shugaba Buhari.
A madadin dokar
Daga nan shugaban kasar ya yi bayani a kan matakan da za su maye gurbin dokar hana fitar.
“Za a kafa dokar hana fitar dare daga karfe 8 na yamma zuwa karfe 6 na safe; hakan na nufin a wannan lokaci za a haramta duk wani kai-kawo sai abin da ya zama lallai da tilas.
“Za a haramta duk wata tafiya da ba ta zama lallai da tilas ba a tsakanin jihohi har sai abin da hali ya yi.
“Za a kyale dakon kayan abinci daga jiha zuwa jiha, shi ma rabi da rabi.
“Sannan za mu tilasta mu kuma tabbatar an saka takunkumin rufe fuska a bainar jama’a baya ga yin nesa da juna da kuma tabbatar da tsafatar jiki.
“Baya ga haka, haramcin da aka saka a kan tarukan jama’a da na ibada suna nan ba a dage su ba”.
Dokar hana fita na nan tukuna
Sai dai kuma game da maganar samar da kyallayen rufe fuskar Shugaba Buhari ya sauke wa gwamnatin tarayya nauyi ta hanyar kira ga gwamnatocin jihohi da kamfanoni masu zaman kansu da masu hannu da shuni su tallafa wa jama’a ta wannan bangaren.
Daga nan sai ya ce domin cire shakku, “dokar hana fita a Yankin Babban Birnin Tarayya da jihohin Legas da Ogun za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar Litinin 4 ga watan Mayu, lokacin da wadannan matakai za su fara aiki”.
Game da Kano
Bayan Shugaba Buhari ya bai wa gwamnatocin jihohi damar yin kwaskwarima ga wadannan ka’idoji da ya furta don su dace da bukatunsu, sai ya ce amma ban da jihar Kano.
“Dangane da Kano”, iniji Shugaba Buhari, “na ba da umarnin tabbatar da dokar hana fita kwata-kwata har tsawon makwanni biyu kama daga yanzun nan.
“Gwamnatin tarayya za ta yi amfani da duk abin da ya kama na ma’aikata da kayan aiki don tallafa wa jihar ta shawo kan kuma ta taka wa annobar birki ta kuma hana yaduwarta zuwa jihohin makwabta”.
Da haka ne kuma ya sanar da karbe iko da dokar hana fita a jihar ta Kano.
Sai dai kuma shugaban kasar bai bayyana me gwamnatin tarayyar ta shirya yi takamaimai ba.
Alamu dai sun nuna lamarin Kano ya fara fin karfin gwamnatin jihar, har ma Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta juya wa Kanawa baya, sannan wasu mutane da kungiyoyi a jihar suka yi kira ga Shugaba Buhari ya sa baki kafin abubuwa su kai inna naha.
Wannan ne dai jawabi na uku da shugaban kasar ya yi tun bayan da annobar coronavirus ta barke a Najeriya.