✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin Rasha da Turkiyya na ganawa a Iran

Tattaunawar ta ranar Talata za ta hada da Ayatollah Khamenei da kuma Ministan Harkokin Wajen Syria, Faisal Mekdad.

Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, sun isa birnin Tehran inda za su tattauna da Shugaban Iran, Ebrahim Raisi.

Bayanai sun ce a hukumance dai makasudin karbar bakucin wannan ziyara da shugaban na Iran ke yi wa Putin da Erdogan, shi ne duba halin da ake ciki dangane da rikicin Syria.

A baya dai kasashen uku sun yi ta tattaunawa a game da rikicin kasar ta Syria, inda Rasha da Iran ke goyon bayan gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.

Tsawon shekarun kuma da Syria ke fama da yaki, a nashi bangaren Shugaba Erdogan na Turkiyya, goyon bayansa na bangaren masu adawa ne da gwamnatin ta Assad.

Ziyarar ta birnin Tehran dai, ita ce ta biyu da Shugaba Putin na Rasha ke yi tun bayan kaddamar da yaki da ya yi a kan kasar Ukraine cikin watan Fabrairu.

Kafofin watsa labarai sun rawaito duk da cewa dai babu batun yakin na Ukraine a ajandar taron, ana dai ganin ta yiwu shugabannin su dubi batun a lokacin ganawar tasu.

Shugabannin uku hadi da Shugaban addini a Iran, Ayatollah Khamenei da kuma Ministan Harkokin Wajen Syria, Faisal Mekdad za su halarci tattaunawar a Talatar nan.

Tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin shawo kan Fadar Kremlin ta yaye takunkumin da ta sanya na ratsawa da kayan abinci zuwa Ukraine ta Tekun Black Sea.