✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Jami’ar ABU ya mika ragamar jami’ar ga Mataimakinsa

Shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Ibrahim Garba, ya mika ragamar shugabancin jami’ar ga mataimakinsa na sashen karantarwar jami’ar, Farfesa Danladi Amodu-Ameh a…

Shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Ibrahim Garba, ya mika ragamar shugabancin jami’ar ga mataimakinsa na sashen karantarwar jami’ar, Farfesa Danladi Amodu-Ameh a matsayin shugaba mai rikon kwarya.

Farfesa Ibrahim Garba, ya mika ragamar gudanarwar ne a ranar Juma’a yayin taron hukumar gudanarwar ta jami’ar.

Shugaban, wanda wa’adinsa zai kare a ranar 30 watan Afrilu 2020, ya yi kira ga mutanen jami’ar da su bai wa sabon shugaban rikon kwarya cikakken goyon baya wajen gudanar da ayyukansa.

A kwanakin baya ne aka ruwaito cewa, rikici ya barke tsakanin shugaban da kuma babbar majalisar gudanarwar jami’ar lokacin da suka bukaci ya ajiye mukaminsa domin daukan hutun shi na barin aiki ranar 1 ga watan Mayu 2020, bayan wata wasika da Rajistaran jami’ar A. A. Kundila ya rattabawa hannu.

Shugaban dai ya yi watsi da batun a karon farko,inda ya jaddada bukatarsa ta ci gaba da zama har sai karshen wa’adin na shi. Za’a iya tunawa dai a watan janairu, an zabi tsohon mataimakinsa, Farfesa Kabir Bala a matsayin wanda zai gaje shi a bayan karewar wa’adinsa a ranar 1 ga watan mayu, 2020.

Daraktar Hulda da jama’a na jami’ar, Dakta Ismail Shehu ne ya tabbatar da mika ragamar gudanarwar jami’ar, inda ya yi nuni da cewa an yi hakan ne saboda kaucewa rigingimu da kuma nuna biyayya ga babbar Majalisar Gudanarwar Jami’ar.