Wata Kotun Majistare dake zamanta a unguwar Fada a Zariyan jihar Kaduna, ta yankewa wata ma’aikaciyar Jami’ar Ahmadu Bello, Ebong Joy, hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari.
Kotun ta kuma aike da diyar matar, Inyene Akpan, wacce daliba ce a ajin karshe a jami’ar, itama hukuncin daurin watanni shida a kurkukun.
- Buhari ya karbi bakuncin shugaban Nijar, Bazoum a Abuja
- Ramadan: Zakzaky ya raba kayan abinci ga mabukata daga gidan kurkuku
Alkalin Kotun, Mai Shari’a Abdullahi Maigamo dai ya sami matar ne da laifin hadin baki wajen shirya garkuwa da ’yartata.
A bayanan wata takardar kotun da wakilinmu ya gani, an gano cewa Misis Akpan ta shirya garkuwa da diyar tata ne sannan daga bisani ta dawo tana zargin abokan hamayyarta a siyasar Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i ta Najeriya (SSANU), reshen jami’ar.
Wadanda ta zarga da garkuwa da diyar tata bayan ta boyeta dai sun hada da Muhammad Gimba Alfa da Mohammed Inusa da Lawal Yakubu Hunkuyi da Haruna Mohammed da Salisu Isa da kuma Rabaran J. F Bukkah; dukkansu ma’aikatan jami’ar.
To sai dai bayan binciken ’yan sanda da kuma sauraron hujjoji a gaban kotun, Mai Shari’a Maigamo ya sami matar da ’yarta da laifin aikata dukkan zarge-zargen da ake yi mata guda uku.
Daga nan ne sai aka yanke musu hukuncin daurin ko kuma zabin biyan tarar N25,000 da kuma N75,000 a karkashin sassa na 97(2) da 140 da na 152 (2) na Kundin Dokar Penal Code na jihar Kaduna na 1991.
Takardun kotun har-ila-yau sun ce an fara gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban Kotun Majistare dake unguwar Chediya, kafin daga bisani a mayar da shari’ar zuwa kotun ta Fada ita kuma ta yanke hukuncin.