✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Shirin tallafa wa masu kananan sana’o’i zai kawo ci gaba’

An bayyana shirin gwamnatin Jihar Kano na tallafawa masu kananan sana’o’i zai kawo ci gaba ta fannin tattalin arzikin al’umma da kuma bude sabbin hanyoyin…

An bayyana shirin gwamnatin Jihar Kano na tallafawa masu kananan sana’o’i zai kawo ci gaba ta fannin tattalin arzikin al’umma da kuma bude sabbin hanyoyin samar da ayyukan dogaro da kai musamman a wannan lokaci da ake ciki.

Wannan bayani i ya fito ne daga bakin Manajan Bankin ba da Rance ga Masu kananan Sana’o’i na Dambatta wato (Dambatta-Makoda Microfinance Bank), Alhaji Inuwa Sa’id Dambatta a wata zantawa da ya yi da wakilinmu, inda ya bayyana shirin a matsayin wata sabuwar hanya ta taimaka wa al’ummar yankunan karkara domin su kara bunkasa sana’o’insu.
Ya ce gwamnatin da ta gabata ta zo ta tarar bankunan ba da rance ga masu kananan sana’o’i kadan ne a fadin jihar, inda ta yi kokarin kara bankuna guda 37 domin kowane yanki ya samu damar yin hulda da cibiyoyin kudi a kusa, wanda kuma hakan ya zamo alheri musamman a wannan lokaci da ake na bukatar samar karin hanyoyi kamar yadda gwamnati ta zo da tsari mai gamsarwa na taimakawa masu kananan sana’o’i a fadin Jihar Kano.
Har ila yau, Alhaji Inuwa ya ce kudin da ake bayar wa rance, yana da kyau al’uma su sani cewa sai an mayar da abin da aka karba ne zaa a samu damar bai wa wadansu domin a tabbatar kowa ya samu tallafin bunkasa sana’arsa ta hanyar wannan shiri, sannan ya tabbatar da cewa bankin ba da rance ga masu kananan sana’o’i na Dambatta zai yi bakin kokarinsa wajen ganin al’umar wannan yanki sun ci moriyar shirin kamar yadda manufofin kafa bankunan suke.
Dangane da mutanen da suka cancanci samun wannan tallafi, Alhaji Inuwa Sa’id Dambatta ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano ta ba da sharuddan irin jerin mutanen da suka kamata a baiwa, kuma dukkan masu neman karin bayani za su iya tuntubar bankunan ba da rance ga masu kkananan sana’o’i da ke kusa da su domin su fahimci yadda shirin yake, inda kuma daga karshe ya nuna matukar jin dadinsa bisa yadda al’umman wannan yanki suke bai wa wannan banki na su hadin kai a duk lokacin da wani shiri ya bullo, tare da fatan cewa tattalin arzikin kasar nan zai ci gaba da bunkasa.