’Yan kasuwa daga wasu jihohin Najeriya sun bayyana takaicinsu na rashin samun ciniki da walwa a wannan lokaci na dokar hana fita a wasu jihohin. Aminiya ta tuntubi wasu ’yan kasuwan musamman masu kananan jari kamar haka:
Jihar Oyo
Mai sana’ar yadi
Al’ummar musulmi za suyi sallar bana cikin wani irin halin kuncin rayuwa da basu taba ganin irinsa ba kamar yadda wani dan kasuwa ya bayyanawa Aminiya.
Alhaji Rabe Mai Yadi ya ce, “Tun farko da ma mutane suna cikin damuwar rayuwar rufe kan iyakokin kasa sai ga matsalar annobar Coronavirus ta shigo wacce tasa mahukumta daukar matakin hana zirga-zirga domin gujewa yaduwar cutar.
Wannan ne yasa cinikin da muka saba yi a baya ya yi kasa sosai a yanzu.
Misali
Wani magidancin da ya saba kashe kudi Naira dubu 20 domin sayan yadukan dinkin kayan Sallah ga ‘ya’yansa yanzu da kyar da jibin goshi zai iya kashe naira dubu biyar.
Ka ga harka ta ja baya ga mai saye da mai sayarwa kenan” inji Rabe Mai Yadi
Jihar Katsina
Yadda farashin kayan miya ke sauki a wasu yankunan jihar
Duk matsalar tattalin arzikin da ake fama da shi, ga batun kullen hana yaduwar cutar coronavirus gami da matsalar harin ƴan bindiga da Jihar Katsina ke fuskanta.
Sannan ga hada-hadar cefanan Sallah bayan kawo karshen azumin watan Ramadan, hakan bai hana samun sauki da kuma ci gaba da saye da sayarwar musamman kayan miyar abincin Sallah wadanda su ne kan gaba a irin wannan lokacin.
Malam Dahiru na daga cikin wadanda ke sayar da kayan miyar ya kuma baiyana cewa, “Saukin da aka samu a bana ya fi na bara nesa ba kusa ba.
Sannan kuma an samu wadatar kayan fiye da bara irin wannan lokacin. Ka ga, bara solon buhun tattasai an sayar da shi sama da naira dubu 10 amma bana tsadar shi naira dubu biyar da dari biyar.
Babban kwandon tumatiri a bana ana sayar da shi naira dubu 10 sabanin bara har dubu 20.
Ita kuwa albasa an sayar da ita naira dubu 6, amma bara sai da ta kai dubu 12″in ji Dahiru mai cefane.
Dokta Gambo da muka rutsa yana sayen kayan miyar ya ce, gaskiya shi kan shi abin ya bashi mamaki a irin yadda ya tarar da kayan miyar suka yi saukin da ba a yi zato ba.
Dukkan wadannan kayan miya an noma su anan cikin Jihar Katsina a yankunan Daura da yankunan Mai’aduwa da kuma Mashi.
Jihar Kaduna
Sana’a na ya kusa kufce mun saboda rashin fita
Malam Abdulmaliki Musa mai saida takalma a kasuwar Tudun Wada Zariya, ya ce dan kada sana’arsa ta kufce mai shi yasa ya dawo kufar gidansa da sana’ar sa na sai da takalma.
Abdulmaliki Musa ya ce kusan mako tara ke nan da kulle kasuwarmu da muke sana’a a cikinta domin wai bullar cutar coronavirus, tun ana bude mu a ranaku biyu a mako sai hakan ya gagara akama rufe kasuwar gaba daya aka ce babu ranar budewa.
Sai su kuma masu sana’o’in kayan abinci aka ce su koma filayan makarantun anguwanninsu, domin suce gaba da Sana’ar su, a can kuma san nan suma ba wai a kullum ba a’ a’ sai ranaku biyu ne kawai aka yarda da su fiyo a mako.
To kaga kamar ni da nake irin wannan sana’ar a bara cikin wannan makon na azumi, nayi shiga garin Kano domin saro kaya ko naba da sako ya kai kusan 20 kuma na sami alheri sosai, kuma kasan dama mu a lokaci irin wannan Sana’ar mu tafi tafiya kuma lokacin ne muke samun amfani sosai to sai gashi wannan karon mun sami akasi sai dai kawai Allah ya bamu mafita.
Kuma bacin da Allah yasa na fara sana’ar a gida to ai da jarina ya kare, kuma ga iyali ga shi babu wani sana’a da mutum zai yi tunda karfi ya fara karewa.
Abdulmaliki ya kara da cewa kuma yanzu maganar da ake ciki babu wadda ya san ranar da zamu fita daga wannan halin da muka sami kanmu a ciki sai Allah, dan haka muna rokon Allah ya kawo mana saukin rayuwa ya bamu mafita amin.
Jihar Sakkwato
Jingine sana’ar na yi sai yau na fito inyi hada-hadar sallah- Mai nama
Wani matashi mai sana’ar sayar da nama a a birnin Sakkwato Mustafa Faruku ya ce wannan cutar coronavirus ta taba masa kasuwanci domin ya shafe wata bai fito ba sai a yau daren Sallah ya yi hada-hadar Sallah.
Ya ce, masa yana suna zuwa gwargwado kafin wannan lokacin amma da naga sun yi kasa a halin rayuwa dole naja baya a hasarar da nake tafkawa.
Faruku ya kwashe shekara uku yana sana’ar sayar da nama a agashe da danye bai taba fashin fitowa ba sai a wannan karon domin lamarin yana cin jarinsa ne ba ya samun riba, sai ya ga zaman gida yafi wannan wahalar kafin abubuwa su canja.
Jihar Bauchi
Alhaji Abubakar Sani Shugaban kungiyar ’Yan Gwari na Jihar Bauchi
A halin da ake ciki farashin kayan gwari ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin jihar Bauchi saboda karancin kayan.
Shugaban kungiyar ’yan gwari na jihar Bauchi Alhaji bubakar Sani, ya sanar da haka azantawar da ya yi da Aminiya “ A yanzu kayan ya yi sauki na lambuna da ake yi a Jihar Bauchi, yanzu an fara ruwan sama a yanzu duk wurin ya jike da ruwa a yanzu kayan tudu muke samu muje wata jiha mu sayo.
Duk da an hana tafiya ana samu a kanananan hukumomin Kirfi da Jama’are da Toro, kaga tattasai akwai a Dass da Toro ama duk ya kare yanzu, tarugu ne da mota namu ya kare wanda zaizo kuma bai zoba don sai damina, kuma kaga ba halin tafiya saboda wannan cutar coronavirus da mukan dauki kaya har Legas har Fatakwal amma yanzu masu sayan kayan nada yawa amma babu kayan wanda wannan ya durkusar da mutanenmu da yawa.”
Ya roki gwamnati data taimaka musu domin samun farfado da sana’ar tasu, saboda a baya suna samu su kai jihohin makwabta dana nesa amma yanzu ba halin haka.