✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shirin Gidan Badamasi kashi na 5 ya zo da sabon salon burge ’yan kallo

Amma gaskiya ba mu ji dadi ba a lokacin da aka ce mana ba za a ci gaba da shirin ba.

Masu kallon shirin barkwancin nan mai dogon zango na gidan Talabijin din Arewa 24 mai suna Gidan Badamasi sun bayyana farin cikinsu da fitowar kashi na 5 da aka fara nunawa a ranar 6 ga Watan Oktoban da muke ciki.

Idan za a iya tunawa da yawa daga masu kallo sun dauka shirin barkwancin ba zai ci gaba ba bayan karewar kashi na 4.

Makonni kadan bayan karewar kashi na 4 ’yan kallo da dama sun fara tambayar ko za a ci gaba da shirin a sakamakon jita-jitar da ke yawo cewa, masu shirya fim din sun bayyana cewa bisa wasu dalilai shirin ba zai ci gaba ba, alhali ba a ji bakin ta bangaren mashirya fim din ba don ba su ce komai a kai ba.

Sai dai ba a je da nisa ba masu kallo suka cika da doki da shauki a yayin da Daraktan shirin Falalu Dorayi ya bayyana a kafar sada zumunta cewa, sun ci gaba da daukar Kashi na 5 na film din Gidan Badamasi.

Labarin barkwancin ya ginu ne a kan tataburzar da ake tafkawa a gidan wani attajiri mai suna Alhaji Badamasi, inda duk da kasancewar gidan masu kudi ne, amma ake ta faman cakwakiya.

A cikin shirin an nuna Alhaji Badamasi (Magaji Ibrahim Mijinyawa) a matsayin matsohon attajiri wanda ke matukar son kudi da mata.

Ya yi aure-aure a cikin shirin, inda ya tara yara da uwayensu suke daban-daban. An yi ta daukaka shirin da inganta shi tun daga kashi na 1, ta yadda masu kallo ba za su so su ga an canza yadda ake tafiyar da fim din a kashi na 5 ba, musamman wajen nishadantarwa da ilimantarwa da kuma fadakarwa.

Wani mai bibiyar shirin mai suna Abba Pele ya ce, an yi matukar kokari wajen rike fim din ba tare da kaucewa daga tushen labarin ba.

“An yi kokari sosai wajen rike shirin ta yadda yake rike da masu kallo ba tare da an kauce labarin ba har zuwa kashi na biyar.

“Amma gaskiya ba mu ji dadi ba a lokacin da aka ce mana ba za a ci gaba da shirin ba.

“Mun yi matukar damuwa saboda shi ne fim din da za ka kalla kai da iyalinka hankali kwannce babu wata fargaba a cikin gidajen al’ummar Hausawa.”

Gidan Badamasi shiri ne wanda daya daga cikin masu taka rawa a ciki ya shirya kuma ya ba da umurni, wato Falalu Dorayi.

Yana daya daga cikin shirye-shiryen da ke jan zare a tashar Arewa 24.

Mashiryin shirin Falalu Dorayi ya fito ne a matsayin Taska, wanda yake mataimaki ne na musamman ga Alhaji Badamasi.

Shi ma wani masoyin shirin mai suna Hassan Safiyanu ya ce ya amfanar sosai, “baya ga nasarar da aka samu a kashi na farko da wadanda suka biyo baya, mun kasa mun tsare muna jiran mu ga yadda za ta kaya a kashi na biyar.

Kuma muna fatan za mu ga abubuwan da muke tsammani ba akasin haka ba,” inji shi.

A daya daga cikin tallace-tallacen kashi na 5 na shirin da masu shirya fim din suka nuna yana gwada zai kasance mafi kyau daga sauran kashe-kashen.

Kamar yadda Falalu Dorayi ya bayyana cewa, sun ba ’yan wasa daban-daban sababbin rawar da za su taka a ciki, sabanin wadda aka fi sanin su da ita, don karin armashin fim din da kuma kayatar da masu kallo.

“Bisa ga irin korafe-korafe da fatan alheri da muke samu, ’yan wasa da sauran ma’aikatan shirin sun zage damtse sosai wajen ganin sun yi amfani da gyare-gyare da shawarwarin da masu kallon shirin ke aikowa, inda hakan ya fito karara a cikin kashi na 5 kamar yadda za a gani.

Kofarmu a bude take don karbar shawarwari kuma mun yi amfani da hakan a kashi na 5 wanda muke sa ran zai fi sauran inganci,” inji shi.

Wani dan wasa a cikin shirin barkwancin, Tijjani Asase, wanda ya fito a matsayin surukin Alhaji Badamasi ya ce, masu kallo za su dara sosai kuma za su ji dadin kashi na 5 din da zarar an sake shi a akwatunan talabijin.

%d bloggers like this: