✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirin Gandun kiwo

A makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta bayar da sanarwar shirye-shiryen kafa gandayen kiwon dabbobi a sassan kasar nan a kokarinta na tsugunar da Fulani…

A makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta bayar da sanarwar shirye-shiryen kafa gandayen kiwon dabbobi a sassan kasar nan a kokarinta na tsugunar da Fulani makiyaya tare da rage rikicin da ke yawan aukuwa a tsakanin makiyaya da manoma. Ministan Aikin Gona da Raya Karkara, Cif Audu Ogbeh ne ya bayar da wannan sanarwa a wajen wani taron bita ga ma’aikatan ma’aikatarsa. Ya ce daga cikin dabarun da za a dauka akwai bullo da hanyoyin inganta samar da irin shanu ta hanyar kimiyyar zamani.

“Muna son mu magance wannan matsala ta kiwon shanu da rikici a tsakanin manoma da makiyaya tare da kawo karshensa,” inji Ogbeh

 Ya kara da cewa “Ba za a ci gaba da barin al’ada ba, don kawai ita al’ada ce alhali tana cutarwa, wajibi ne mu yi mata gyara. Muna magana ne a kan gandun kiwon shanu ba gidajen gona na kiwon shanu ba.”  Duk da cewa gwamnati ba ta yi cikakken bayani a kan gandun ba, ya bayyana cewa gandun kiwon dabbobin da ake shirin kaddamarwa sun fi gonakin kiwon shanu girma kuma za su kunshi gine-gine da suka hada da makarantu da asibitoci da kasuwanni.

 Jihohi da dama sun yi alkawarin bayar da filaye don samar da maslaha kan wannan batu. “Jihohi 16 sun ba mu filaye mu yi aiki a kansu; aikin ba zai kasance mai araha ba,” inji Ministan. Kuma ya nuna cewa makiyaya sun hada kai da ma’aikatarsa a kan wannan shiri. “Duk lokacin da muka tattauna da makiyaya kullum sukan ce idan muna da ruwa da ciyawa ba za mu je ko’ina ba.” Sai dai tuni wasu sassa na kasar nan sun fara adawa da wannan shirin. Misali Gwamnan Jihar Abiya, Okta Okezie Ikpeazu ya ce jiharsa tana da karancin fili don haka rashin adalci ne ga manomansa a bayar da fili ga “baki su mamaye.” Ya ce: “Ba mu da isasshen fili don yin noma don haka mutanenmu suna bukatar karin fili ne.” 

Haka ma wata kungiyar Yarbawa mai suna Gamayyar ’Yan Kishin Yankin Yarbawa (ONAC) ta bayyana irin wannan ra’ayi tare da yin gargadin cewa “ba za su bayar da ko inci daya na kasar Yarbawa ba.” Shugaban da ya fuskanci wannan shiri da dabi’ar sanin ya kamata shi ne Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong. Ra’ayinsa a kan wannan dama ta damar kasuwanc shi ne: “Muna magana ne a kan gonakin kiwo. Kuma muna magana a kan bunkasa kiwon shanu, don haka b azan yi amfani da kalmar ‘hanawa’ domin in fara korar mutane da suke da sha’awa a kai ba.”

Idan aka dauki fassarar Lalong ta harkar kasuwancin, kuma haka lamarin yake, to ba za a samu tilasci a cikin shiga harkar ba. Misali a bar jihohin da suke son shiga a fara da su, kuma a kyale jihohin da suka botsare, su ga alfanun haka daga sakamakon da zai biyo baya. Idan shirin ya samu nasara jihohin da suka kakkafa gandun kiwon shanun za su fara nuna amfanin da suke samu ga jihohin da ba su yi ta hanyar samun cikakken zaman lafiya da kyakkyawar mu’amalar jama’a da bunkasa harkokin kasuwancin da arahar nama da madara da ganda.

Idan gandun kiwon shanun ya kankama ya yi kyau, yana nufin za a kara samun kudin shiga ga jhohin da suke gudanar da shi. Yana da muhimmanci a wannan lokaci mu fahimci cewa wasu jihohi suna adawa da shirin ne jim kadan da kashe-kashen da suka auku a Jihar Benuwai da wasu wurare. Muna da yakini fusata da dacin ran za su sauka ta yadda dukan bangarorin za su dawo su zauna su kalli shirin gandun kiwon shanun a matsayin kyakkyawar dama kuma mafita ta karshe ga matsalar da take damun kasar nan.

Yana da muhimmanci a nuna cewa wajibi ne a kara kokari wajen tsarawa da aiwatarwa a magance matsalolin muhalli da sauran matsalolin da za su taso daga kashin dabbobin a gandun. Domin baya ga dimbin kashin da za su yi, shanu suna fitar da gas mai yawa sakamakon hanyoyin narkewar abincin da suke ci ke gudana. Dukan wadannan ya kamata a yi amfani da su wajen gudanar da wasu ayyukan masana’antu da Amfanin gidaje ciki har da samar da wutar lantarki da taki. Wani batun da ya shafi muhalli shi ne na iskar da  dabbobin za su samar, wannan za a iya magance shi ta hanyar daddasa itatuwa masu yawa a duk zagayen gandun kiwon shanun.

Muna taya Gwamnatin Tarayya da Ministan Aikin Gona kan kokarin nemo mafitar kuma muna bukatar su ci gaba da shi ba tare da bata lokaci ba.