’Yan Sanda a Jihar Bauchi sun sha alwashin hukunta masu neman kawo matsala a zaben kananan hukumomin jihar da zai gudana ranar Asabar.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Lawal Jimeta ya ce rundunar ta kammala shiri domin ganin jam’iyyu da masu zabe sun samu aminci a lokacin zaben.
- Buhari ya taya Sarkin Bauchi murnar cika shekara 50
- Gwamnan Bauchi ta dage dakatarwar da ya yi wa Sarkin Misau
Ya ce rundunar ba za ta raga wa duk dan bangar ziyasa ko dan daban da ta kama yana kokarin tayar da rikici ba.
Sanarwar ta kuma ce wajibi ne a kiyaye dukkannin matakan kariyar COVID-19 a tsawon lokacin zaben.
Lawal Jimeta ya kuma sanar da hana zirga-zirgar ababen hawa daga karfe 12 dare na ranar Juma’a zuwa karfe 2 na ranar Asabar.