✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shiri domin gamuwa da Allah (7)

Mu na yi wa Allah Madaukakin Sarki godiya domin yawan alheranSa zuwa gare mu. Duk da kasawarmu, Allah bai bar mu mu kadai ba, amma…

Mu na yi wa Allah Madaukakin Sarki godiya domin yawan alheranSa zuwa gare mu. Duk da kasawarmu, Allah bai bar mu mu kadai ba, amma Ya kare mu daga cikin dukan jarrabawar Shaidan, Ya kuma kawo mu wannan rana cikin masu rai da lafiya. Wannan abin godiya ne kwarai da gaske.
Kamar yadda muka yi magana a makon jiya, akwai lokacin da masu bi za su taru a gaban dakalin shari’ar Ubangiji Allah, su ba da lissafin abin da duk suka yi yayin da suke raye cikin wannan duniya; za mu kuma bayyana a fili duk abin da muka yi ko nagari ko mugu, domin wannan ne fa maganar Allah ta yi mana wannan kashedi a cikin Littafin Romawa 14 : 10 – 13 wadda take cewa “Kai fa don mene ne kake zartar wa dan uwanka? Kai kuma, don me ka raina dan uwanka? Gama dukanmu za mu tsaya a gaban kursiyin shari’a na Allah. Gama an rubuta, bisa ga raina, in ji Ubangiji, a gare ni kowace gwiwa za ta durkusa, kowane harshe kuma za ya yabi Allah, kowane dayanmu fa za ya kawo lissafin kansa ga Allah. Kada fa mu kara zartar wa juna: amma gwamma ku zartar haka, kada kowa ya sa abin tuntube a cikin tafarkin dan uwansa, ko kuwa dalilin faduwa.”
A matsayinmu na masu bin Yesu Kiristi, dole ne mu fuskanci wannan  ranar shari’a, dole mu tsaya a gaban wannan dakalin shari’a na Yesu Kiristi domin mu karbi ladan abin da muka yi yayin da mu e cikin wannan duniya. Maganar Allah na koya mana cikin Littafin 2Korinthiyawa 5:10 cewa “Gama dole dukanmu za mu bayyana a gaban dakalin shari’a na Kiristi, domin kowane daya ya kawo sakamakon aikin da ya yi cikin jiki, ko nagari ko mugu.” Wannan shi ne abin lura a cikin rayuwarmu ta yau da kullum, wannan ranar da dole kowane dayanmu ya bayyana a gaban Ubangiji Allah, haka nan kuma daidai da daidai za mu zo mu furta da bakinmu duk abin da muka yi – ko mai kyau ko kuwa mara kyau.
Idan kuwa wannan al’amari haka yake; shin wane irin shiri ne ya kamata kowane mai Bin Yesu Kiristi ya yi?  Wace irin rayuwa ne ya kamata mu masu bi mu yi a cikin wannan duniya yayin da muke da sauran lokaci? Wadanne irin ayyuka ne ya kamata mu aikata yayin da muke raye cikin wannan duniya kafin mu fuskanci Allah a rana ta karshe?
Yesu Kiristi ya yi magana a cikin Littafin Matta 5 : 13 – 16, maganar Allah na cewa “Ku ne gishirin duniya, amma idan gishiri ya rabu da zakinsa, da me za ya gyaru? Nan gaba ba ya da amfani ga komai ba, sai a zubar, a tattake karkashin sawun mutane. Ku ne hasken duniya. Birni da ke kafe bisa tudu ba ya boyuwa. Kuma ba a kan kunna fitila a sa ta karkashin akushi ba, amma bisa teburi sai ta haskaka wa dukan wadanda ke cikin gida. Haka nan ku kuma, bari haskenku ya haskaka gaban mutane domin su ga ayyukanku masu kyau, su girmama Ubanku Wanda ke cikin sama.”
Yesu Kiristi ya kwatanta rayuwar masu bin sa da gishiri da kuma haske. Wadannan abubuwa biyu suna da muhimmanci sosai a rayuwarmu ta yau da kullum. Gishiri yana da amfani da yawa, musamman ma ba da dandano ga miya ko abinci; akwai abubuwa da dama da ba za ka iya ci ka ji dadinsu ba idan ba a sa gishiri a ciki ba. Ma’ana shi ne idan ba ka sa gishiri ko da kadan a cikin wasu irin abinci ba, babu yadda za ka ji dadin cin irin wadancan abincin koda yaya kanshin abincin yake. Iyayen a da; idan suna so su yi ajiyar nama, kuma ba sa son naman ya lalace, ko ya rube, sai su samo gishiri, su shafa a jikin naman da suke son su busar, ko su yi ajiyarta, muddin sun yi wannan, to, ba wani tsutsar da za ta shiga balle naman ya yi wari; haka kuma ma naman ba zai rube ba, ashe gishiri yana hana ruba, yana hana abu yin wari. Da an shafa gishirin, zai janye ruwan da ke jikin naman har ya bushe.
Yesu Kiristi Ubangijinmu ya ce – “Ku ne gishirin duniya; abin da ya kamata mu tambayi kanmu shi ne, shin wace irin rayuwa ne muke yi cikin wannan duniya da muke ciki? Wane irin dandano ne rayuwarmu ta kawo ga mutanen da suke kewaye da mu? Muna cikin mawuyacin zamani yanzu, muna ganin yadda al’umma suke lalacewa, muna ganin rubar da ke kewaye da mu a yau da kullum; wane irn canji ne rayuwar ta kawo ga rayuwar wadanda ke cikin kazanta har yanzu? Mene ne muka yi game da wadanda rayuwarsu take wari domin ayyukan zunubi? Idan da gaske kai ko ke gishiri ne kamar yadda Yesu Kiristi ya ce, babu shakka duk inda ka shiga za ka bar gurbi mai kyau domin wadansu su yi koyi da halayenka masu kyau. Lokacin da ka tsaya a gaban Yesu Kiristi, daya daga cikin abin da za ka amsa shi ne ko rayuwarka ta kawo caji cikin rayuwar mutanen da ke kewaye da kai, ko ka yi rayuwar banza ce kawai. Yesu Kiristi ya sake cewa “Mu ne Hasken Duniya”: masu magana sukan ce haske maganin duhu; duk inda akwai duhu, idan ka kawo haske me zai faru?
Duhu zai bace nan take, babu dogon lokaci, duk inda akwai duhu, idan har haske ya bayyana, to debe shakka duhu zai tafi nan take. Haske da duhu ba sa tafiya tare, haka ba zai yiwu ba, dole daya ya bar wa dayan wuri. Kuma idan duhu ne ke wurin sai haske ya bayyana, dole ne duhu ya tafi, domin duhu ba zai iya ja da ikon karfin haske ba. Mene ne hasken rayuwa ga masu bin Yesu Kiristi? Yesu ya ce ku bari haskenku ya haskaka a gaban mutane domin su ga ayyukanku masu kyau, su girmama Ubanku Wanda ke cikin sama – ashe hasken nan kyawawan ayyukanmu ne da muke yi, da wadansu mutane sukan iya gani.
Mutum mai kirki ba za ya boyu ba ko kadan. Ayyuka masu kyau ga mutane abu ne da yake faranta wa Allah rai sosai. Duniya a zamanta na yanzu, tana cikin duhu sosai; Shaidan ya sa mutane suna ta sabon Allah, Shaidan ya kawo abubuwa da dama ya sa cikin tunanin mutum, a yau mugunta ba komai ba ne; kisa ba komai ba ne; a yau mugunta ta yi tsanani sosai; a ganina mun riga mun fi Sodom da Gomorah yin mugunta; a wancan lokacin Allah Ya shar’anta su nan take, Ya yi mauu ruwan kibiritu, ruwan wuta, ya kona su duka har da dabbobinsu.
A yau, alherin Allah ne kawai ya sa ba mu hallaka ba. Mu sani fa idan muna tafiya cikin duhu, kuma ba mu tuba ba har ranar da Yesu Kiristi zai zo, zai zama abin kaito. Mu sake binciken kanmu – da gaske ne kai din nan gishirin duniya ne kamar yadda Yesu Kiristi ya ce? Da gaske ne haskenka yana haskakawa kamar yadda Yesu Kiristi ya umurta? Sai mu yi tunani sosai mu kuma gyara tafiyar mu.  Za mu ci gaba mako mai zuwa daga nan.