Kamar yadda muka yi bincike makon da ya shige; muka ce idan Allah Ya yarda yau za mu ci gaba da koyarwar da muka soma. Muna magana ne a kan Shari’a wadda za a yi wa masu bin Yesu Kiristi, mu koma inda muka yi karatu makon jiya daga cikin Littafin 1Korithiyawa 3 : 7 – 15 wanda yake cewa “Domin wannan fa shi wanda ya dasa ba wani abu ba ne, ko shi wanda ya yi ban ruwa kuma, sai Allah Wanda ke ba da amfani. Yanzu fa da mai dasawa da mai ban ruwa daya ne: amma kowane za ya samu nasa lada gwargwadon wahala tasa. Gama mu abokan aiki na Allah ne, ku kuwa gonar Allah ne, ginin Allah ne. Ni kuwa bisa ga alherin Allah da aka ba ni, kamar magini mai gwaninta, na kafa gindi; wani kuwa yana tada gini a kai, Amma sai kowane mutum ya yi hankali irin gini da yake yi a kai. Gama ba wanda yana da iko ya kafa wani gindi daban da wanda an rigaya an kafa ba, Yesu Kiristi ke nan. Amma idan kowane ya yi gini bisa gindin nan, ko zinariya, ko azurfa, ko duwatsu masu daraja, ko itace, ko ingirci, ko tattaka; aikin kowane mutum za ya bayyana: gama ranar nan za ta tone shi, da yake cikin wuta za a gwada ta, wuta kuwa da kanta za ta gwada aikin kowane mutum, na kowane iri ne. Idan aikin kowa da ya gina a kai ya tsaya, za ya karbi lada. Idan aikin kowa ya kone, za ya sha asara, amma shi da kansa za ya tsira; amma sai ka ce ta wurin tsakiyar wuta.”
Ina so mu gane wani abu sosai domin shi ne zai zama tushen gane wannan koyarwa, a cikin makonnin da suka gabata, mun yi magana a kan fyaucewa da za a yi wa masu bin Yesu Kiristi daga cikin wannan duniya, maganar Allah kuma ta koya mana cewa sai wadanda suke a shirye ne za su samu a fyauce su, duk wanda ba ya da dangantaka tsakaninsa da Yesu Kiristi, kada ma ya yi tsammanin zai tafi tare da shi a lokacin, wannan ba zancen zuwa coci ko masujada ba ne, ba kuwa zancen wai kana kiran kanka Kirista ban ne, ko kuwa kana ji kamar domin an haife ka a cikin gidan masu bin Yesu Kiristi ba, ba kawai domin an yi maka baptisma ba ne, domin akwai mutane da yawa a yau a cikin ekklisiyoyi ko kwa coci-coci wadanda kowane Lahadi suna zuwa sujada amma gaskiyar ita ce, ba su da dangantaka tsakaninsu da Yesu Kiristi Ubangijinmu. Su dai sun tashi ne suna ganin iyayensu suna zuwa coci (Majami’a); haka suka girma suna gani, zuwa coci kawai ba ya mai da mutum ya zama Kirista, abin da zai kawo mutum cikin wannan zumunci ko kuwa dangantaka da Yesu Kiristi, shi ne ban-gaskiya cikin shirin ceton da Allah Ya kawo ga dukan duniya, wanda ta cika yanzu ta wurin zuwan Yesu Kiristi cikin wannan duniya, ya mutu bisa gicciye, aka bizine shi, bayan kwana uku ya tashi daga matattu, domin ya wanke mu daga zunubanmu, wannan ita ce hanya kadai da za ta kawo mu cikin wannan dangantaka, muddin ba ka furta wannan shaidar ban-gaskiya da bakinka ba, ba ka da rabo cikin masu bin Yesu Kiristi ko da kana kiran kanka mai bin Yesu. Yesu Kiristi ya yi magana a cikin Littafin Matta 7: 21 – 23, cewa; “Ba dukan mai ce mini, Ubangiji, Ubangiji, za ya shiga mulkin sama ba, sai wanda ke aikata nufin Ubana wanda ke cikin sama, a cikin wannan rana mutane da yawa za su ce mini, ubangiji, ubangiji, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, da sunanka kuma muka fitar da aljanu da sunanka kuma muka yi ayyuka masu iko? Sa’annan zan furta musu ban taba saninku ba dadai, rabu da ni, ku masu aikata mugunta.” Mu gane cewa kawai domin ka iske kanka cikin masu zuwa Majami’a domin sujada bai isa ya sa ka shiga cikin mulkin Allah ba; amma kamar yadda maganar Allah ta ce a inda muka karanta a aya ta 21; Ba dukan mai ce mini Ubangiji, Ubangiji, za ya shiga cikin mulkin sama ba, sai wanda ke aikata nufin Ubana wanda ke cikin sama. Akwai bambanci tsakanin kiran sunan Ubangiji Allah; da kuma yi masa biyayya. Kowa ma zai iya cewa Ubangiji Allah, amma ba kowa ba ne zai yi maSa biyayya
Aikata Nufin Ubana Wanda Ke cikin sama: Wannan shi ne abin da Allah zai shar’anta yayin da muka sadu da shi cikin sama. Sai mu lura da wannan, bayan an fyauce masu bin Yesu Kiristi daga duniya, Lokacin wahala da tsanani zai soma na shekara bakwai, wadanda an raba su kashi biyu, wato shekara uku da rabi, sashi na farko, lokaci ne mai wahala kwarai ga dukan mazaunan wannan duniya, akwai kuma sauran shekara uku da rabi mai tsananin wahala a kan dukan mutanen da ke cikin wannan duniya. Mu tuna fa da cewa an rigaya an fyauce masu bin Yesu Kiristi, a lokacin irin kungiyar da ake ce da ita Majalisar dinkin Duniya za ta tashi domin ta yi kokarin magance abin da ya shafi al’ummar duniya da ta sa mutane da yawa sun bace kawai ba tare da wani cikakken bayani ba. Majalisar dinkin Duniya za ta yi kokari ta kwantar da hankulan mutane; amma na dan lokaci ne kawai. A daidai lokacin nan ne kuma masu bin Yesu Kiristi wadanda aka rigaya an fyauce za su fuskanci shari’a a gaban dakalin shari’a na Yesu Kiristi. Wannan shari’a ba domin ceto ba ne, a’a dukan wanda aka fyauce to, ya tsira, amma akwai zancen lada da wannan mutum zai karba gwargwadon aikin da ya yi a wannan duniya. Bisa ga yadda mutum ya yi wannan ne za a ba shi ladansa.
A cikin Littafin 1Korinthiyawa 4 : 1 – 5, maganar Allah tana cewa, “Mu fa sai a yi lissafinmu haka nan, Ma’aikatan Kiristi ne, wakilai na asirin Allah kuma, daga nan kuwa abin da ake nema ga wakilai, a iske su da aminci. Amma ni, ba wani abu ba ne a gare ni in samu kwankwanto a hannunku, ko a hannun mutum: har ba ni kan yi wa kaina kwankwanto ba. Gama ban san wani aibi a kaina ba, koda haka wannan ba ya sa na barata ba: amma mai yi mini kwankwanto Ubangiji ne. Domin wannan kada a shar’anta komai da garaje, kafin Ubangiji wanda za Ya tone boyayyun al’amura na duhu, Ya bubbude shawarwarin zukata a sarari; sa’adda kowane mutum za ya samu nasa yabo daga wurin Allah.”
Zan so in ci gaba da bayani daga wannan wuri mako mai zuwa idan Mai duka ya bar mu cikin masu rai. Ubangiji Allah Ya taimake mu, amin.
Shiri domin gamuwa da Allah (6)1
Kamar yadda muka yi bincike makon da ya shige; muka ce idan Allah Ya yarda yau za mu ci gaba da koyarwar da muka soma.…