✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin za ka so a yi da ’yar uwarka?

Masallacin Abu Hanifa Ra’as Tanurah, SaudiyyaHuduba ta farko Gabatarwa:Bayan haka, Abu Umamah (RA) ya ba mu labari kan wani wurin tsayuwa mai ban mamaki da…

Masallacin Abu Hanifa

Ra’as Tanurah, Saudiyya
Huduba ta farko

Gabatarwa:
Bayan haka, Abu Umamah (RA) ya ba mu labari kan wani wurin tsayuwa mai ban mamaki da neman da ba a saba ba. Wani abu ne ya faru a wani majalisin daga majalisin Annabi (SAW0 sahabbai sun hadu a wurin mafi alherin mutane, kamar taurarin da suka kewaye wata, suna koyon addini da kyawawan halaye da kyautatawa daga gare shi, labarin sama yana zuwa musu da shiriya da rahama da imani, yana ba su labari kan Aljanna da wuta kamar suna ganinsu kiri-kiri, sai ga wani saurayi ya shigo musu yana cewa: “Ya Rasulullah! Ka yi min izini in yi zina, ” Subhanallah yaya cikar kyawawan dabi’un Annabi (SAW), yaya girman imanin wanna saurayi!
Amma kyawawan dabi’un Annabi (SAW) a fili suke wajen tawali’unsa da tausayinsa da rahamarsa ga dukkan halitta, shi ya sa har saurayin zai iya tsayawa a gabansa ya nemi wannan bukata daga gare shi ba tare da taraddadi ko kunya ba, Allah Ya yi gaskiya cikin fadinSa: “Saboda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma da ka kasance mai fushi kai kaushin zuciya da sun watse daga gare ka. Sai ka yafe musu laifinsu, kuma ka nema musu gafara, kuma ka yi shawara da su a cikin al’amarin. Sa’a nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dogara ga Allah. Lallai ne Allah Yana son masu tawakkali.” (k:3:159).
Da yawa mu iyaye da malamai da masu tarbiyya da masu da’awa muna bukatar wadannan siffofi a cikin dabi’unmu, domin hakan yana jefa tunani a cikin zukatan ’ya’yanmu da dama.
Amma imanin saurayin nan a fili yake cikin abubuwa biyu:
Na farko: Gudunsa ga haram da nesantarsa ga zunubi, yana nufin ba zai auka wa zina ba, har sai ya nemi izinin Manzon Allah (SAW) don ya zamo halal, yaya zai samu haka bayan Allah Madaukaki Ya ce: “Kada ku kusanci zina, lallai ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga zama hanya.” (k:17:32).
Na biyu: Lallai shi ya zo neman magani ga zuciyarsa daga likitan zukata.. domin a cikin fadinsa: “Ya Manzon Allah! Ka yi min izini in yi zina…” kamar yana kokawa ne ga Annabi (SAW) kan halinsa cewa: “Hakika na kai makura wajen son yin zina har ban iya bice shi daga zuciyata ta yadda zai zama halal kamar shan ruwa, don haka nake neman hallata shi daga gare kafin ya bata min addini da duniyata.”
Sai mutane suka taso masa suka kama yi masa fada suna cewa: “Rufe baki mana.. rufe mana baki!” “Ku kusanto da shi, sai ya zo kusa da shi,” sai ya zauna.
Ya kusanto da shi domin amintar da shi, ya zaunar da shi domin ya natsu.. wannan daya ne daga cikin hanoyin farko na magani, domin shi yana bukatar tausayawa da rahama. Sa’annan ya ce masa: “Za ka so a yi da mahaifiyarka?” Ya ce: “A’a wallahi Allah Ya sanya ni fansar gare ka.” Sai (SAW) ya ce: “To su ma mutane ba su so a yi da iyayensu mata.” Sannan ya ce: “Za ka so a yi da ’yar uwarka?” Ya ce: “A’a wallahi, Allah Ya sanya ni fansar gare ka.” Sai (SAW) ya ce: “To su ma mutane ba su so a yi da ’yan uwansu mata.” Sai ya ce: “Za ka so a yi da gwaggonka?” Ya ce: “A’a wallahi, Allah Ya sanya ni fansar gare ka.” Sai (SAW) ya ce: “To su ma mutane ba su so a yi da gwaggoninsu.” Sai ya ce: “Za ka so a yi da innarka?” Ya ce: “A’a wallahi Allah Ya sanya ni fansar gare ka.” Sai (SAW) ya ce: “To su ma mutane ba su so a yi da innoninsu.”
La’ilaha illalah! Tattaunawa ta hankali tana ceto hankalin da ya kauce wa hanya, muhawara ta natsuwa tana shiga kwaryar zuciya, duk wadda za ka yi zina da ita imma ta kasance uwa ko ’ya ko ’yar uwa ko gwaggo ko innar wani mutum ne irinka mai kishi, yana kin a bata masa mutunci koda zai kai ga jefa shi a cikin kabari.
Yana da kyau ku ji a jikinku kamar yadda wannan saurayi Musulmi ya ji, shi yana munin wannan mujirimanci da wani mujirimi ya aikata shi da wata muharramarsa, me ya fi wannan muni.. babu zuciya mai kyau da za ta yarda da haka koda a mafarki ne.. to yaya wannan abu mai radadi da daci zai auku a zahiri, gara ya kasance tare da ita a cikin kasa (kabari) da ya zauna a bayan kasa.
Sai ya ce: “Sai (SAW) ya dora hannunsa a kansa ya ce: “Ya Ubangiji Ka gafarta zunubinsa, Ka tsarkake zuciyarsa, Ka katange farjinsa!” A bayan haka wannan saurayi bai sake komawa zuwa gare shi ba – ma’ana bai sake sha’awar zina ba balle ya aikata.”
Kubutarwa daga hallaka da jinya da warkarwa.. magani ya sauka a kan wurin cuta, tausasawa da munakasha da gamsarwa da addu’a. Duk hakan ya auku ne a majlisin cikin ’yan dakikai, wanda ya zo zina ce mafi soyuwa a gare shi sai ga shi ta koma abu mafi ki a zuciyarsa.Tsarki ya tabbata ga Mai jujjuya zukata. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga likitan gyara zukata.”
Ya kai saurayi! Idan ya kasance wancan saurayi yana fadin wadannan kalamai duk da karancin abubuwan da suke yada zina a zamaninsa, me za ka ce a wannan zamani wanda abubuwan da suke ingiza mutum ga aikata zina suka yawaita fiye da baya? Ga karuwai nan sun zamo hajojin sayarwa barbaje a fili a birane da dama suna kara-kaina! Ga hotuna masu motsi da marasa motsi na mata tsirara ga yaduwar hanyoyin halatta zina! Mata na bayyana tsaraicinsu da bayyanar da adonsu da cudanya da maza a yayin tafiye-tafiye! Ga raunin imani da kwaikwayar kafirai da fajirai! Ga jinkirta yin aure ga tsananta kudin da ake kashewa kafin a yi aure! A daidai lokacin da wutar sha’awa take kankama a tsakanin samari da ’yan mata kamar wutar daji! “Ido yana zina, zinarsa kallo, hannu yana zina, zinarsa shafa, kafa tana zina zinarta tattaki, harshe yana zina, zinarsa furuci, baki yana zina, zinarsa sumba. Raina yana buri da sha’awa, farji yana gaskata wannan ko ya karyata su.” Harshe yana kuwwa ya ku masu hankali! Mene ne mafita?
Allah Ya taimake ka ya kai saurayi! Lallai nauyin da ke kanka babba ne. Abin da ke gabanka muhimmi ne kuma babba. Ka kiyaye Allah, sai Ya kiyaye ka! Ka kiyayi Ubangijinka, ka runtse ganinka, ka tsare farjinka, ka yi aure idan za ka iya aure, ka yi azumi idana za ka iya azumi. Ka shagaltar da kanka wajen yin ayyuka masu amfani koda wasanni masu amfanarwa, kada ka sanya wan kanka lokacin da ba ka yin komai ya zamo mai yawa. Kashedinka da zuwa wuraren fitina da barna, ka guji mugun aboki mai aikata barna. Ka sani wanda ya nemi kame kansa Allah zai kare shi.”
Kamun kai na daga cikin sabubban kwaranye bakin ciki, kuma daga cikin mutum uku da falalen dutse ya rufe a kogo akwai mutumin da ya ce: “Ya Ubangiji! Ka san cewa lallai ne ni ina da wata ’yar Baffana wadda na fi so a cikin mata, sai na neme in yi zina da ita amma ta ki, face na ba ta Dinari dari, sai na nema har na samu, na zo gare ta na ba ta, na samu kanta, yayin da na daidaita a tsakanin kafafunta, sai ta ce: “Ka ji tsoron Allah kada ka sanya zobe ba bisa muhallinsa ba! Sai na mike na bar mata Dinari darin. Idan Ka san na aikata haka ne domin tsoronka Ka bude mana (kofa) sai Allah Ya bude musu (kofa) suka fice.”
Idan ka ga taimako daga Allah wajen kiyaye sha’awa to ka sani lallai kai kana cikin bayin Allah Madaukaki wadanda aka zabe su akan tsarkake su. “Kuma wadda yake a cikin dakinta ta neme shi ga kansa, kuma ta kukkule kofofi, kuma ta ce, “Ya rage gare ka!” Ya ce “Ina neman tsarin Allah! Lallai Shi ne Ubangijina. Ya kyautata mazaunina. Lallai ne shi masu zalunci ba su cin nasara. Kuma lallai ne ta himmantu da shi. Kuma ya himmantu da ita in ba domin ya ga dalilin Ubangijinsa ba. Kamar haka dai , domin Mu karkatar da mummunan aiki da alfasha daga gare shi. Lallai ne shi daga bayinMu salihai yake.”
Allah Ya yi min albarka da kuma ku a cikin Alkur’ani Mai girma, kuma Ya amfanar da ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi da zikiri mai hikima. Ina fadin wannan magana tawa ina neman gafarar Allah gare ni da ku da sauran muminai daga dukkan zunubi, ku nemi gafararSa ku tuba gare Shi, lallai Shi Mai gafara ne Mai jinkai.