✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin ko Labour za ta bayar da mamaki a Arewa ta Tsakiya?

Addini ya yi matukar tasiri a zaben Shugaban Kasa.

A Jihar Filato, zaben na gwamna da za a yi nan da mako, ana tunanin zaben na gwamna da Majalisar Jihar, zai zama daban.

Ita dai Jihar Filato, kamar yadda masu lura da harkokin siyasar jihar suka yi bayani, kan wannan takara ta kujerar gwamnan jihar ‘yan takarar jam’iyyu uku ne suke kan gaba a wannan takara.

Wadannan ‘yan takara, sun hada da Dokta Patrick Dakum na Jam’iyyar LP da Caleb Mutfwang na Jam’iyyar PDP da kuma Nentawe Yilwada na Jam’iyyar APC.

Wadannan ‘yan takara guda uku wadanda dukkansu suka fito daga shiyar tsakiyar jihar, biyu daga cikinsu suna da goyan bayan daya daga cikin tsofaffin gwamnonin jihar.

Misali, Dokta Patrick Dakum na Jam’iyyar LP yana da goyan bayan Tsohon Gwamnan Jihar Cif Joshua Dariye.

Shi kuma Caleb Muttwang na Jam’iyyar PDP yana samun goyon bayan Jonah Jang shi kuma Nentawe Yilwada na Jam’iyyar APC yake samun goyan bayan gwamnan jihar mai ci, Simon Lalong.

Masu lura da harkokin siyasar sun yi bayanin cewa idan aka dubi sakamakon zaben Shugaban Kasa da Majalisun Tarayya da ya gabata, inda Jam’iyyar LP ce ta fi samun kuri’u a jihar, za a iya cewa LP din za ta bayar da mamaki a zabukan na gaba.

Sai dai kasancewar Jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben kujerun sanatoci guda biyu a cikin guda uku, kuma ta kasance kan gaba wajen lashe zaben kujerun Majalisar Wakilai a jihar, hakan ya sa masu lura da harkokin siyasar suke hasashen cewa ’yan takarar wadannan jam’iyyu za su iya samun gagarumar nasara, a wannan zabe da za a gudanar.

Har ila yau masu lura da harkokin siyasa sun yi hasashen cewa ita ma Jam’iyyar APC duk da ta zo na uku a zaben da ya gabata, dan takarar ta na kujerar gwamna, zai iya samun gagarumar nasara, musamman idan aka dubi umarnin da Majalisar Musulmin jihar, ta ba al’ummar Musulmin jihar na su zabi dan takara na Jam’iyyar ta APC a zaben.

Haka kuma kasancewar Gwamna Lalong ya fadi takararsa ta sanata, ana tunanin hakan zai sa ya kara dagewa wajen ganin ya kawo dan jam’iyyarsa, wanda ya tsayar domin ya gaje shi duk da cewa jam’iyyar na fama da rikicin cikin gida.

Yanzu dai lokaci da sakamakon wannan zabe ne kawai, zai nuna mana wanda zai lashe wannan zabe.

A Jihar Nasarawa, jihar da gwamna mai ci da tsofaffin gwamnoni guda biyu duka suke rike da mukami, inda Sanata Abdullahi Adamu yake shugabantar APC, shi kuma Sanata Tanko Almakura yake sanata, duk da ya sha kaye a zaben da ya gabata, amma duk da haka jam’iyyar APC ta sha kaye a zaben Shugaban Kasa.

Masu bibiyar siyasar jihar suna ganin akwai sabani da rashin jituwa a tsakanin masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar APCn jihar, wanda hakan ya sa Kungiyar Concern APC Stakeholders ta shirya taron manema labarai, inda a ciki ta yi kira ga Gwamna Sule ya yi duk mai yiwuwa wajen hada kan jam’iyyar kafin zaben na gobe.

Sai dai addini ya yi matukar tasiri a zaben Shugaban Kasa, inda wasu Kiristocin jihar suka bayyana cewa a adalci bai kamata Musulmi ya gama mulki, sannan wani Musulmi ya karba ba.

Wani mazaunin Lafiya mai suna Moses Buba ya ce ko kadan bai yi da-nasanin zaben LP ba, domin a cewarsa, duk da APC ta mayar da takara Kudu, amma ba ta ba Kirista takarar ba.

A Jihar Binuwei, Gwamnan Jihar mai ci wanda dan Jam’iyyar PDP ne ya tsayar da Mista Titus Uba, wanda ya yi alkawarin ciyar da jihar gaba ta hanyar habaka harkokin noma.

Sai dai yadda Jam’iyyar APC ta lashe zaben Shugaban Kasa da yadda Gwamna Samuel Ortom ya sha kaye a zaben sanata, hakan wata manuniya ce cewa akwai aiki a gaban shi zaben samun wanda ya tsayar ya yi nasara a zaben gwamna.

A wani kokari da gwamnan ya yin a jawo hankalin masu kada kuri’a, gwamnan ya dage dokar hana hawa Babura a yankin Sankera, wanda ya kunshi kananan hukomomin Katsina-Ala da Ukum da Logo Haka kuma gwamnan ya nuna goyon bayansa ne ga dan takarar Shugaban Kasa ta LP, wato Peter Obi, duk da cewa bai samu nasara a jihar ba.

Dan takarar APC a jihar, Rabaran Hyacinth Alia yana matukar tayar da kura a siyasa a jihar, wanda kuma nasarar APC a zaben na mako biyu da suka gabata ta sa ya kara saka ran cewa akwai nasara.

A dayan bangaren kuma, dan takarar Labour, Herman Hembe shi ma yana ganin akwai nasara, musamman ganin yadda a siyasar bana ake kallon jam’iyyar a matsayin ta Kiristoci.

A Jihar Neja, za a fafata ne tsakanin dan takarar PDP, Alhaji Isah Liman Kantigi da dan Majalisar Wakilai, Umar Bago na APC da dan takarar Labour, Mista Joshua Bawa.

Dan takarar APC na Shugaban Kasa, Bola Tinubu ne ya lashe zaben jihar, sannan gwamnan jihar mai ci, Abubakar Sani Bello ya lashe zaben sanata a daidai lokacin da takwarorinsa suka sha kaye ya sa magoya bayan APC suke yi wa zaben kallon nasara.

Sai dai dan takarar PDP na Jihar, Alhaji Isah ya shirya matuka, sannan kasancewar har yanzu Tsohon Gwamnan Jihar, Mu’azu Babangida Aliyu yana da karfi a siyasar jihar, ya sa yake tunanin samun nasara.