✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin ko akwai cutar sata a jerin cututtukan dan Adam?

Likita, wai akwai cutar sata? Kuma wai ba mutum ne ke sa kansa ba. To yaya take, kuma mene ne maganinta?Daga M. Hussain, Ruma Amsa:…

Likita, wai akwai cutar sata? Kuma wai ba mutum ne ke sa kansa ba. To yaya take, kuma mene ne maganinta?
Daga M. Hussain, Ruma

Amsa: Haka ne, domin kuwa akwai cutar da kan sa mutum halin bera, wadda a kimiyyance ake kira Kleptomania. Abin da hakan ke nufi kuwa shi ne mutum ya rika daukar abin da ba ya bukata ta hanyar dauke-dauke. Wato ke nan sai idan ba ya bukatar abin da ya dauka din. Idan yana da bukatar abin da yake dauka din to wannan sata ce tsagwaro ba rashin lafiya ba. Ita wannan rashin lafiya an kasa ta ne cikin cututtukan kwakwalwa masu sa naci.
To ta yaya akan gane mutumin da ya dauki wani abu wanda ba nasa ba cewa ba ya bukatarsa? Akwai hanyoyi da dama, misali mutum ne ma’aikaci mai karbar albashi mai dan tsoka duk wata, ya je masallaci da takalmi mai kyau amma ya buge da kwasar takalma masu araha a buhu, kuma ba wai sayarwa zai yi ba, kawai dai sai ciwon ya motsa. Ana samu wannan matsala jefi-jefi cikin al’umma, domin akwai mutane fitattu musamman a turawa wadanda ma suke da alaka da sarauta da aka san suna da wannan matsala.
Masu wannan matsala ba satar ce kawai ake gani a tare da su ba, a’a har wasu alamu na rashin lafiyar kwakwalwa kamar kadaici, zullumi, shaye-shaye da sauransu.
Idan aka ga wani ya fara nuna irin wannan alamu ke nan ba zama za a yi a zura masa ido ba, magani za a nema masa, domin akwai maganin, a asibitin kwakwalwa. Sai dai kamar yadda muka fada, wanda ke da dan hali wanda ba shi da cin yau, balle na gobe, ba ya cikin masu irin wannan cuta. Yawaitar kyamarori a wuraren taruwar jama’a ma kamar kasuwanni kan saukaka matsalar.

Shin yawan mantuwa yana da alaka da wata cuta ne a kwakwalwa ko kuwa?
Daga Bin Malik

Amsa: E, akwai mantuwar da take ta yau-da-kullum ce, wadda aka fi cewa sha’afa, misali mutum ya manta mukullin gidansa a ofis, ko ya manta yana da daurin aure a kauyensu washegari. Shi ma wannan sau daya a sati ko sati biyu ba matsala. Amma a ce kullum mutum shi sai ya yi mantuwa kuma shi ba tsoho ba, to a gaskiya sai an binciki lafiyarsa. Domin a tsofaffi sosai akan samu irin wannan yau-da-gobe kusan kullum
To akwai kuma babbar mantuwa, irin mantuwar da mutum zai manta sunan wani nasa, kamar matarsa ko dansa, ko ya manta wane gari yake ciki, ko wane wata ake ciki, irin wannan ko a tsoho ne ba saurayi ba, ana ganin shi ma alamu ne na ciwon mantuwa, kuma yana nufin akwai babbar matsala a kwakwalwa, don haka sai mutum ya je, ko a kai shi asibiti a binciki kwakwalwar.

Me ke kawo yawan tofar da miyau ne?
Daga Anas Kasim

Amsa: To ita ma dai wannan matsala kamar yadda mutane da dama suke aikowa watakila za a iya saka ta a rukunin kananan matsalolin kwakwalwa. Ya kamata masu yawan tofar da yawu da kaki haka kawai a wurare barkatai, wurare wadanda ma ba na kazanta ba, su san cewa yawan hakan, mutum ya yi, ya yi , ya kasa bari, zai iya kasancewa daga kwakwalwa ce matsalar, saboda jimirin tofarwar ko da yaushe kan iya sa kwakwalwar ma ta saba.
To amma shi sabo na kwakwalwa ya kamata a san cewa kafin a ce an bar shi rana daya zai yi wahala, sai mutum ya hada da wasu dabaru, kamar koyawa kansa yawan hadiyar miyau akai-akai, tunda a jikinmu ake sarrafashi me zai sa mu kasa hadiyeshi. Sai kuma mutum ya rika yawan shan ruwa, da yawan cin cingam maras suga, da yawan tsotsar alawa da yawan aswaki da sauransu. Abubuwa dai wadanda za su daukewa kwakwalwar wannan tunani na tofe-tofe ba gaira-ba-dalili.

Wai shin me ke sa tashin zuciya ne? Ni ina da matsalar na je asibiti an ba ni magani amma har yau ba a dace ba.
Daga Aminu Gezawa

Amsa: Akwai abubuwa da dama da kan sa tashin zuciya, tun daga matsalolin ciki da hanji, da hanta, har na jiki baki daya. Misalan matsalolin ciki da hanji da kan sa tashin zuciya sune gyambon ciki ko olsa, da shigar kwayoyin cuta cikin hanji, da duk wata matsala da za ta shafi hanta. Cutukan jiki kuma da kan iya kawo matsalar sun hada da zazzabin tafot, da na maleriya da farko-farkon alamun ciwon sankara da na ciwon koda da dai sauransu.
Ka ce ka je asibiti an ba ka magani amma ba mu ji ka ce ga irin gwaje-gwaje da aune-aune da aka ba ka don a gano ainihin inda matsalar take ba.

Me ke sawa wasu komin cin su ba sa kiba? amma wasu ko abin sha suka sha za a gansu tubarkallah?
Daga Ashiru D. Gwarzo

Amsa: Akwai abubuwa da dan dama da kan sa abinci ya zauna ya kuma amfani jikin mutum. Na farko shi ne aminci da ingancin abin. Akwai na’uin abinci wadanda da mutum ya ci suke narkewa, ko kuma a yi amfani da shi wajen kara kuzari, nau’in carbohydrate, wanda shi muka fi ci. nau’in protein ya fi zama a jiki ya kuma fi ratsa sassan jiki, da dadewa kafin narkewa.
Sai kuma batun gado. Ko da mutum na cin abinci nau’i mai gina jiki ko mai maiko idan ba shi da wani mai jiki a danginsa to shi ma da kyar ne yayi jiki. Akwai kuwa na’in wasu mutane wanda jikinsu ke saurin kona abinci. Ko me suka ci yanzun nan jikinsu zai kona shi, ya ki zama. Wadanna su muke kira fast metabolisers.
Akwai kuma samun cututtuka wadanda suke zuke albarkacin abincin da mutum ya ci, kamar kanjamau, tarin fuka, amai da gudawa, tsutsar ciki da dai sauransu.

Na ga bayaninka game da yawan fitsari a rana. Ni na auna bai kai yawan lita 2 ba. Ko akwai matsala?
Daga Mustapha KGS

Amsa: To tambayar da kai ma zan maka a nan shi ne, ko shin kana auna yawan duk wani abu mai ruwa da kake sha a rana, tun daga na karin kumallo har zuwa kwanciya? Idan ka auna ka ga bai kai ba, watakila abin da kake sha ne bai taka-kara-ya-karya-ba.