✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin da Hamisu Breaker Rakiya Moussa ta yi soyayya?

Mece ce asalin abin da ke tsakanin Rakiya Moussa da Breaker? Ga abin da muka sani

Tun farkon makon jiya da Hadiza Gabon ta saki tsakuren bidiyon tattaunawarta da jaruma Rakiya Moussa, sai aka fara magana a kan irin soyayyar da jarumar ta yi da za a iya makauniya.

Bayan an saki cikakkiyar hirar, sai kafofin sadarwa suka dauki zafi inda da dama suka tausaya wa jarumar tare da fatan alheri.

A gefe guda kuma, wasu na bayyana kiyayya da zargi a kan wanda ta so hakan.

A cewarta a hirar, ta so shi a da lokacin ba shi da daukaka, amma yanzu daukaka ta zo masa, amma sai ya kyale ta.

Da aka tambaye ta ko za ta iya mantawa da shi, sai ta ce har ta mutu ba za ta daina son shi ba.

Wannan ya sa ake alakanta lamarin soyayyar da mawaki Hamisu Breaker.

Wace ce Rakiya Moussa

Rakiya ’ya ce a wajen fitaccen mawaki, Moussa Poussy, wanda ya shahara matuka a kasar Nijar.

Ya kasance ciki ko kuma jagoran kungiyar mawaka ta Takeda ta Jamhuriyar Nijar tare da mawaka Adams Junior da Fati Mariko da Sa’adu Bori da John Sofakole da Mamoudou Abdousalam da Sani Aboussa da Yacouba Moumouni da sauransu.

Rakiya ta fi yin fice a wakokin bidiyo na soyayya, inda take yawan fitowa tare da Hamisu Breaker da Garzali Miko da Auta MG da Kb International da sauransu.

Shin Hamisu Breaker ne?

Da Hamisu Breaker da Rakiya Moussa duk jaruman tsagin Tamil ne, karkashin jagorancin Darakta Sanusi Oscar 442.

Haka kuma akwai fitattun jarumai irinsu Mommee Gombe da Garzali Miko da Kb International da sauran jarumai. Sannan Amina Amisco wadda ita ake kira Maman Tamil.

Rakiya ta yi wakokin bidiyo na soyayya da Garzali Miko da Hamisu Breaker, sannan ta shaku da su biyun sosai, da kuma Kb da Auta MG, wanda shi ma dan kasar Nijar ne.

Wani mai suna Mu’az Sulaiman Sa’eed, wanda ya ce shi makwabci ne kuma kaman wa yake a wajen Hamisu Breaker ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa shi ganau ne a soyayya tsakanin Hamisu Breaker da Rakiya Moussa.

A cewar shi, ya san lokacin da Rakiya ke zuwa gidan su Hamisu Breaker, inda har shi take gaishe shi har da tsugunawa saboda ta ga yadda Hamisu yake girmama shi.

Sai dai ya ce a iya sanin shi, ba ya tsammanin Hamisu ya so Rakiya, amma dai lallai ya ga alama cewa Rakiya na matukar son shi Hamisun. Amma da alama ta masa son masu wani ne kawai.

Amma da gaske Rakiya take?

Sai dai wasu sun sa shakku a game da batun na Rakiya Moussa, inda wasu suke ganin tamkar dirama ta shirya.

Baban Tamil, Darakta Sanusi Oscar 442, wanda uban gidan Hamisu Breaker ne da Rakiya Moussa din ya bayyana cewa kawai lauje cikin nadi.

Oscar 442 ya wallafa hoton tattaunawar, sannan ya rubuta cewa, “Don Allah waye ya san sunan wannan fim din?”

Wannan tambayar ta Oscar ta tayar da kura, inda mutane da dama suke tsammanin ai idan ma akwai soyayyar, to dole ya fi kowa sani.

A kasan rubutunsa din, jaruma Madam Korede ta kira sunan Hadiza Gabon, inda ta ce darakta wato Sanusi Oscar yana magana.

Sai Hadiza Gabon ta mayar da martani cewa, “ai shi ya san komai ko fim ne ko ba fim ba.”

A wani rubutun, Sanusi Oscar cewa ya yi, “In dai kana namiji ka yi shirmen soyayyar wasan kwaikwayon nan kuka, to ka nemi zanin kanwarka ka daura.”

Ita ma Maman Tamil, wadda ita ce ta fi kusa da Rakiya Moussa da sauran jarumai mata a Tamil din a kasan rubutun Sanusi Oscar da ya tambaya sunan fim din cewa, “Labarin kanzon kurege sunansa.”

Me jaruman Tamil suka ce?

Aminiya ta bibiyi shafin Rakiya Moussa na Instagram, inda a ciki ta ga babu inda ta yi maganar soyayya.

Sai dai a ranar 26 ga Oktoban shekarar 2021, Rakiya Moussa ta saka hoton ta da Garzali Miko, inda ta rubuta cewa, “Ni da mutumina.”

Garzali Miko da Hamisu Breaker ba su ce komai har zuwa lokacin hada wannan labarin.

Sai dai Kb International ya yi martani a kasan rubutun Alhaji Sheshe, inda ya yi tambaya wai wa ye take magana, tambayar sa ta sa mutane suke mamaki kasancewar shi ma dan Tamil ne kuma ya yi wakoki da ita da yawa sannan suna tare da Hamisu da Garzali din da Rakiya baki daya.

Kb International ya ce, “Wai fim ne ko da gaske ne? In dai da gaske ne to Allah Ya sa kaffara ne.”

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Hamisu Breaker, amma wayarsa ba ta shiga.

Aminiya ta tuntubi wani makunsacin Hamisu Breaker da Garzali Miko, amma ya ki cewa komai.