✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin da gaske yawan shan garin kwaki na iya kawo makanta?

Shin da gaske ne yawan shan garin kwaki na iya kawo makanta? Daga Muhammad Musa, Suleja  Amsa: Eh, kwarai haka ne yawan shan garin kwaki…

Shin da gaske ne yawan shan garin kwaki na iya kawo makanta?

Daga Muhammad Musa, Suleja 

Amsa: Eh, kwarai haka ne yawan shan garin kwaki na tsawon lokaci wato shekaru zai iya lahanta idanu domin akwai wata guba ta cyanide a cikin garin da wadansu ba sa iya fitarwa sosai yayin aikin rogon. Ita wannan guba takan iya lalata jijiyoyin laka musamman na ido, gani ya yi rauni. Wannan binciken masana ma ya tabbatar da haka. Wannan bincike wanda aka yi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya an wallafa sakamakonsa a Mujallar Kimiyya ta Abinci ta Afirka ta watan Janairun shekarar 2014.

To me hakan ke nufi? Shi ke nan sai a daina cin garin kwaki? A’a binciken ya yi nuni da cewa sai an dade ana ci yau-da-kullum, ba irin cin nishadi ba, kuma sai ana cin wanda gubarsa take da yawa. Duk da cewa ba ganewa za a yi wanne ne gubarsa ke da yawa ko wanne ne ba yawa ba, an tabbatar dafa kwakin sosai yana iya tasiri a kan gubar. Wato ke nan cin tebar da ta sha wuta sosai ya fi shan danyen gari da ruwa da sukari da wadansu kan yi haka nan.

Ina tambaya ne game da abin da ya shafi tsagewar baki a lokacin zafi. Shin babu wata matsala da hakan za ta iya haifarwa? Kuma yaya mutum zai yi domin magance matsalar?

Daga Nura Muhammad, Gusau

Amsa: Eh bushewar, yanayi ce ke sa bushewar sassan jiki kamar lebba da cikin hanci da tafin kafafuwa. Da damina ta sauka sosai za ka ga abin ya lafa, don haka ba wata matsala. Man basilin kawai za ka rika shafawa zai kiyaye yankewar da fatar wurin ke yi.

Akwai wani magani da mutum zai yi amfani da shi wajen kau da cin-zanzana a fuska?

Daga Aminu Adamu, Malam-Madori.

Amsa: Eh, wadansu za ka ga suna cewa akwai nau’o’in mai masu gyara tabon fata. Wadanda sai an gwada akan san na kwarai, amma mu dai tiyata ake yi a gyara wurin a likitance. Fatar wani wuri za a debo kamar daga cinya a zo a lullube wajen da ita. 

Me ke kawo yawun barci, musamman lokacin da mutum yake sharara barci? Shin ko akwai wani magani da mutum ya kamata ya rika amfani da shi domin rage yawun barcin?

Daga Yaana Garba, Gashuwa

Amsa: Kin san barci kanen mutuwa ne. Wadansu ba sa iya hadiye yawu a yayin barci sai ya taru ki ga yana dalalowa a kan matashi. Ba wani ciwo ba ne bambancin halitta ne. A likitance akwai kwayar magani da kan iya rage dalalowar yawun barci amma bushewar bakin da yakan sa, ba dadi, wadansu sukan gwammace gara ma yawun barcin. 

Ina da jiki amma ba na son cin abinci, ba na cin komai sai ’ya’yan itatuwa da wasu kayan kwadayi. Ko hakan akwai matsala ga lafiyata?

Daga A.D.

Amsa: kwarai kuwa akwai matsala ga lafiyarka tunda ba ka samun ci-maka daidaitacciya kuma ingantacciya. A yanzu da za a binciki jininka za a ga sinadarai wadanda jiki ke bukata don yin aikin yau da kullum irin su ma’adinai da bitaman sun yi kasa saboda ba ka cin isasshen abin da zai kara su a jininka.

Ni kuma ina fama da yawan bugun zuciya da sauri musamman da dare. Ko me ya kamata in yi?

Daga M.A Rinji, Toro da U.S. Mu’azu., Funtuwa da Maman Musty

Amsa: Eh, ba alama ce ta lafiya ba wannan. Idan mutum na samun bugun zuciya da sauri-sauri a kowane lokaci na wuni ko dare, babban asibiti zai je a dubi sababi. Ku a nan Toro watakila sai ka dangana da babban asibiti a Bauchi ko kuma Jos. Ku kuma na Funtuwa watakila sai kun leka Zariya.

Shin mene ne maganin ciwon Sikila?

Daga Bello Aliyu

Amsa: A halin yanzu dai maganin ciwon Sikila shi ne dashen bargon wani marar ciwon. Sai dai aikin da tsada sosai kuma ba a yi a kasar nan. A kwanakin baya idan da kana bin labaru za ka tuna inda aka samu labarin wadansu mata ’yan gida daya masu matsalar da suka je wata kasar Turai aka yi musu dashen bargo, aikin miliyoyin Naira ne.

Wanda ba zai iya wannan aiki ba sai dai a ba shi shawara ya rike magungunan da likitansa ya dora shi a kai sosai da sosai ya rika yawan shan ruwa, ya kuma guji cizon sauro.

Da gaske ne tsakuwa za ta iya taruwa a kafa kamar yadda take taruwa a koda?

Daga Aminu B.K

Amsa: Eh, irin sinadaran da kan taru su zama tsakuwa a koda da matsarmama za su iya taruwa a gwiwa da idon sawu da kan babban dan yatsa ga masu ciwon sanyin kashi na gout amma ba a matsayin tsakuwa ba, sai dai a matsayin allurai. Wato a cikin jiki wadannan sinadarai kamar tsakuwa suke zama, a wajen jiki kuma kamar allurai na gilashi suke zama. Shi ya sa masu ciwon sanyin kashin gout suke jin zafi a gwiwa da idon sawu, a wani lokaci ma zafin kamar ana soka kusa ko allurai.

Ko me ya sa idan mutum yana zazzabi aka yi masa allura sai ya yi hararwa?

Daga Garba Sabiyola, Gashua

Amsa: Akwai magunguna da allurai da dama da aka sani cewa idan aka yi wa mutum za su iya sa wasu ’yan kananan matsaloli kamar tashin zuciya da amai. Amma ba kowa ne ke samun hakan ba. Idan ana yi wa mutum allura ko magani kuma ya san maganin ko allurar suna sa shi amai, ya fada da wuri a canja masa. Ba za a rasa wadda ba ta sa amai ba  a jerin magungunan da ya kamata a ba shi.