✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shin an sake nada Sarki Sanusi Khalifan Tijjaniyya?

Bangaren Sheikh Dahiru Bauchi ya ce ba shi da masaniyar an ba Sarki Sanusi Khalifanci.

Bangaren mashahurin malamin Tijjaniyya, Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya ce ba shi labarin an sake nada Sarkin Kano Muhammadu Sanusi a matsayin Khalifah Darikar a Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan wasu bayanai da ke yawo cewa Shugaban Darikar ya nada tsohon Sarkin Kanon, a taron rufe Tafsiri a garin Kaulaha.

Majiya mai tushe a Zawiyyar Shaikh Dahiru Bauchi ta shaida Aminiya cewa babban dan Shehu Dahiru, “Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru shi ne Shehu Mahiy ya nada a matsayin mai magana da harshensa a Najeriya, bai fada mana wannan batu ba, Dazu ya bar nan zai tafi Umrah, ba shi da masaniya a kanta.

“Kuma bangaren Kaulaha ba su tuntubi Shehi ba, kamar yadda Halifa ya ce, in ma akwai bukata kuma za a yi, tilas sai an zauna da malmai, to ba a zauna da malaman ba tukuna, ba mu da wani labari kan wannan batu.”

Duk kokarin da wakilin Aminiya ya yi na jin bakin Sheikh Dahiru Bauchi, ko Ibrahim ya ci tura.

Tun bayan dawowar Sheikh Dahiru daga Tafsirin da ya gabatar a Kaduna, har zuwa lokacin hada wannan rahoto, bai fito ba, shi kuma Ibrahim yana hanyarsa ta zuwa Umrah.

Amma wata majiya ta ce, “Matsayin Shehi kan wannan batu ba ya sauyawa kuma duk lokacin da ya fadi magana ba ya canja ta.

“Ya kuma yi mana isassu kuma gamsassun bayanai kan wannan batu na matsayin Khalifa, cewa Khalifa na farko Muhammadu Sanusi Sarkin Kano lalura ce ta sa Shehu Ibrahim ya nada shi kan wannan mukami.

“Ya kuma umurci dukkan halifofinsa da almajiransa cewa duk wanda zai ziyarce shi in bai samu hali ba ya ziyarci Sarki Sanusi I, wannan lalurar kuma babu ita a yanzu.

“Sannan Shehu Ibrahim ne kawai ke iya daukar dukkan khalifofinsa da almajiransa ya sanya su a hannun mutum guda, bayan shi babu wanda yake da ikon yin haka.

“Shehi ya ce Tijjaniya hanyace ta Allah zuwa ga Allah, ana samun mukami ne da ilimi da aiki da tsoron Allah, don haka babu bukatar a nada wani mutum a wani mukami don kawai a ce an nada shi, ba haka Tijjaniyya take ba.”

Majiyar ta ce, “A halin yanzu duk cikin Khalifofin Shehu Ibrahim wadanda da suka raga a raye suke kuma da izini maras iyaka kan lamarin Darikar, Shehu Dahiru ne da Sheikh Sherif Ibrahim Saleh.

“Ta ina za ka dauki wadannan bajiman malamai ka sa su a hannun wani? Ai ba zai yiwu ba.”

%d bloggers like this: