Amsa: Eh, a da ne ake hada wadannan allurai a cikin sassan jikin dabbobi irin su birrai da saniyar gida da ta daji da ma aladu. Alluran poliyo ta farko-farko wato shekara 50 zuwa 60 da suka wuce a cikin wani sashe na kodar biri ake hada ta. To da yake ana bukatar sashen jikin wani abu mai rai domin hada allurar, a yanzu ana hada yawancinsu ne a cikin kwan kaji, shi ya sa za ka ji ana tambaya idan mutum ko yaro na da borin jini idan ya ci kwai, to ba za a yi masa wasu nau’ukan alluran rigakafin ba.
Da ma dai wasu magungunan likitancin in ma dai daga sassan tsirrai aka hada su ko a cikin sassan dabbobi, ko kuma a wasu abubuwa da aka kera. Misali kafin a samar da allurar nan ta masu ciwon suga ta insulin daga sassan dan Adam, ai a da da sassan aladu ake yinta.
Ni kuma wani mai ne nake amfani da shin cocoa butter sai na ga yana gyara mini jiki fatata tana kyau sosai. Shi ne nake tambaya ko yana kwaye fata ce, wato bleaching.
Daga Amina A.
Amsa: A’a shi wannan man da man cikin waken koko ake yinsa, kuma kayan cikinsa da kika lissafa babu wanda ke kwaye fata. Don haka shi wannan mai ba na bleaching ba ne yana dai gyara fatar ce.
Matata tana da ciki wata bakwai amma tana yawan shan sukari. Ko hakan matsala ce?
Daga Kabir Sani
Amsa: A’a ba wata matsala in dai ba cewa aka yi tana da ciwon sukari a wannan ciki ba, tunda ba ita kadai ke amfani da shi ba, har da abin da ke cikinta.