Manoman masara a Najeriya sun bayyana damuwa dangane da hukuncin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zartar na bai wa wasu kamfanoni damar shigo da masara daga ketare.
Manoman hatsin na ganin matakin da gwamnatin ta dauka zai yi tasiri a kan farashin masara a kasuwanni musamman a wannan lokaci da aka fara girbinta a gonaki.
Bayan tsawon watanni da masu gidajen gona da hada abincin dabbobi suka shafe suna yi mata matsin lamba, Gwamnatin Tarayya a yanzu ta bai wa wasu kamfanoni hudu damar shigo da tan 262,000 na masara daga waje.
Jerin kamfanonin da Gwamnatin ta bai wa damar shigo da masarar daga watan Agusta zuwa Oktoba sun hadar da WACOT, Chi Farms Limited, Crown Flour Mills, da kuma Premier Feed Mills.
Gwamnatin Tarayya ta bakin Babban Bankin Kasar CBN, ta sauka daga hukuncin da ta gindaya a baya na haramta shigo da kayan abinci daga ketare.
- Jiragen yaki sun ragargaji ’yan bindigar Kaduna
- Harin Kagara: Mun dukufa wajen kare al’ummarmu —Gwamnan Neja
Hakan na kunshe cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan ranar 6 ga watan Agustan 2020 wadda CBN ya aikewa da Hukumar Hana Fasakwauri ta Najeriya.
A halin yanzu dai farashin buhun masara ya tashi daga Naira 19,000 zuwa N21,000 a wasu kasuwannin sayar da hatsi a kasar.
Wani manomin masara a garin Gauraka daura da titin Kaduna, John Isah, ya ce bayar da damar shigo da masara a wannan lokaci da ake shirin fara girbinta babbar damuwa ce.
Ya ce matakin da gwamnati ta dauka na ba da damar shigo da masara daga kasashen waje babban kuskure a wannan lokaci.
Haka kuma wani manomin masara a jihar Nasarawa, Danjuma Ayuba, ya ce bai kamata gwamnati ta ba da wannan dama ba a daidai lokacin da aka fara girbin sabuwar masara.
Shi kuwa wani manomi mai suna Ibrahim Sunday, ya ce adadin masarar da gwamnati ta ba da damar a shigo da ita bai yi yawan da zai yi tasiri a kan farashinta ba a kasuwa.
Sai dai ya ce gwamnatin ba ta yi la’akari da lokacin da ya dace ta zartar da wannan hukuncin ba.
Shugaban Kungiyar manoman masara ta Najeriya, Ibrahim Kabiru, ya ce akwai wauta game da yanke shawarar shigo da masara kuma babu abinda hakan zai haifar sai koma baya.