✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shi ke nan matasan nan sun yi mutuwar banza?

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina (08165270879), mai sharhi ne kan al’amuran yau da kullum, kamar kuma yadda ya kasance Sakataren kungiyar Muryar Talaka na…

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina (08165270879), mai sharhi ne kan al’amuran yau da kullum, kamar kuma yadda ya kasance Sakataren kungiyar Muryar Talaka na Najeriya. A wannan makon, ya yi tsokaci ne game da mutuwar matasa, a yayin gudanar da jarabawar daukar aiki. Ga abin da yake cewa:
Abin da ya faru makon da ya gabata, inda dubban daruruwan matasa suka fito don rubuta jarabawar neman aikin Hukumar Shige Da Fice, sakamakon yawan matasan da suka fito ba tare da hukumar ta shirya abin bisa tsari ba; ya haifar da turmutsitsin da har ya zama ajalin kusan mutum ashirin. Dama masu iya magana na cewa, idan ajali ya yi kira, to ko babu ciwo a je.
Wannan ba shi ne karon farko da masu neman aiki ke rasa rayukansu wajen rigi-rigin rubuta jarabawar da ba ta da tasiri ko amfani ba. A shekarun baya ma hakan ta faru, inda wata hukumar ta sanya matasan gudun fanfalaki cikin zafin rana, mutane suka yi ta mutuwa kuma babu abin da ya faru. Ba a kama kowa daga cikin shugabannin wannan hukuma ba, ba ta’aziyya ko kalamai masu tausasa zuciya daga hukumomi, kazalika babu jami’in gwamnati daya da ya yi murabus sakamakon wannan abin takaici.
Bari in fara da Jarabawa: Ni dai a fahimtata, dalilin rubuta jarabawa shi ne domin a tantance masu hazaka. Koda a makaranta, jarabawa ba za ta amsa sunanta jarabawa ba sai ta hada fannoni guda uku: Na farko fannin kwakwalwa mai nuna kaifin fahimta. Na biyu, fannin halayya, wato bangaren da ke nuna dabi’ar mutum; ladabinsa, mu’amalarsa da sauransu. Da Turanci, ana kiran wannan da ‘Affectibe Domain.’ Fanni na uku shi ne na iya kere-kere kamar zane, abin da ya shafi kera inji ko gyara wasu na’urori da sauran abin da hannu ke iya sarrafawa. Akwai ma batun sarrafa jiki kamar guje-guje da tsalle-tsalle da sauransu. A Ilimance duk malami in ya zo zai shirya tambayoyin jarabawa, to ya kamata ya yi la’akari da wadannan fannoni guda uku, maimakon kawai ya mayar da hankali wajen bangaren tunani ko kaifin basira.
To Amma irin jarabawar da hukumomin gwamnati ko kamfanoni masu zaman kansu ke shiryawa masu neman aiki, jarabawa ce ta rashin hankali, ta keta, wadda haramtatta ce. Akan shirya jarabawa ne kawai don a batar da mutane, ba wai don a auna fahimtarsu ba. Ina mamakin me ya sa mutumin da ya kammala jami’a ko wata kwaleji, ya samu takardar shaidar kammalawarsa za a ce sai an sake jaraba shi? Bayan kuwa shaidar takardar kammala karatunsa ta nuna cewa ya cancanta?
Wani abin lura a nan shi ne, idan har don saboda tabarbarewar ilimi ta sa ake shirya jarabarwar daukar ma’aikata, to yadda ake shirya jarabawar ba zai sa a gane abin da ake so a gane ba; domin shirya ma mutum 68,000 jarabawa a filin wasa hauka ne. Da farko dai ba jami’an da za su iya tsare masu jarabawar, su tabbatar ba su yi satar amsa ba, ko kuma suka dinga kwafar na junansu ba. Don haka jarabawar sam ba ta da wani amfani. Wani abin la’akari shi ne, gyara ita kanta jarabawar ga hukumar da aikinta ba shirya jarabawa ba, ba karamin jidali ba ne.
Wani abin ban haushi shi ne, mutane da yawa ba su yarda ana ma gyara jarabawar ba. Kawai ina-janje-ina-janje suke da takardun bayin Allah. A irin wannan jarabawa, galibi ba a la’akari da me mutum ya karanta. Da wanda ya karanta Hausa da wanda ya karanta Tarihi da wanda ma kimiyyar gine-gine ya karanta ko tsimi da tanadi, duk iri daya ake masu. Idan kuma muka nazarci irin tambayoyin da ake shiryawa, su ma abin ban dariya ne. Misali, za ka ga tambaya a kan wane ne shugaban Hukumar Shige Da Fice ta kasa? Ko mene ne sunan Ministan Cikin Gida da sauran jagaliya?
Idan kuwa jarabawar kamfani ne mai zaman kansa ya shirya ta, misali kamar jarabawar da Hukumar Yi Wa ’Yan kasa Rijista (NIMC) ta taba shirya wa masu neman aiki. Kodayake an yi amfani da na’ura mai kwakwalwa wajen shirya jarabawar to amma tambayoyin baki dayansu sun saba wa ka’ida jarabawa, domin tambayoyi ne da suka shafi mutanen da suka kware da lissafin duna. Bayan kuma mutanen da za su yi aiki da hukumar, kamata ya yi a ce wadanda suka karanci bangaren Fasaha ne ba Kimiyya ba. To haka duk ma’abocin neman aiki a Najeriya yana sane da ire-iren wadannan irin jarabawa, wadanda sam ba su dace a kira su da jarabawa ba.
Takaici goma da goma, yau a ce dan Najeriya in zai nemi aikin gwamnati sai ya biya kudi! Abin da kowane mai neman aikin shige da fice ya biya shi ne Naira dubu. An ce a kalla sama da mutum miliyan shida suka cike takardun neman aikin. Idan muka tara wadannan kudade za mu ga miliyoyin Naira hukumar ta samu daga mutanen da ba su da tabbas din cin abinci sau uku a rana. Idan kuma muka yi magana sai a ce ai haraji ne, bayan kuma wasu ne za su sace kudin su biya wa matansu da kannensu bukata.
Domin su kara muzguna wa bayin Allah, haka za su  gayyaci mutane ba za su ba su ko ruwa ba. Mutane za su kwashi uwa duniya su ta fi, wasu ma sai sun ciwo bashin kudin mota, wasu in sun samu sun kai kansu wurin da za a yi jarabawar sai dai su kwana a waje ko masallaci ko wani kango, kuma daga karshe ba a dauke su aikin ba.
Tunda ake shirya wannan jarabawar zalinci har yau ba a taba hukunta masu shirya jarabawar ba saboda yadda suke take hakkin jama’a. Shi ya sa yanzu kowace hukumar gwamnati sai ta labe da daukar aiki ta cuci ’yan Najeriya.
Yau ga shi Abba Moro, Ministan Al’amuran Cikin Gida yana kalaman banza, duk da rashin da aka yi amma shi matsalarsa it ace ya ci gaba da rike kujerarsa; duk kuwa da rashin iya aikinsa. A lokacinsa ’yan Najeriya mun ga masifu iri-iri, domin duk ma’aikatun da ke karkashin hukumarsa babu wadda ba a kama da abin fallasa ba ko kuma sakacin aiki. Huikumar Cibil Defense su ma a baya an kama su da badakalar sayar da takardun daukar aiki. Jami’an Kwastam sun bari ana ta shigo da haramtattun kaya. ’Yan sanda ba su aikinsu yadda ya kamata, sai a je gari guda a kashe duk mutanen garin, a sake dawowa gobe a maimaita ba tare da an dauki matakin komai ba kuma duk lokacin want ton minister amma wai har yana da bakin da zai yi magana.
Yanzu dai matasan Najeriya sun fara ji a jikinsu. Ko dai su share masallaci ko kuma su share kasuwa. Ma’ana, ko su cire tsoro da raggwanci su shiga gwagwarmayar neman ’yanci kamar yadda matasa ke yi a wasu kasashe ko kuma su ci gaba da zaman walakanci tare da yin mutuwar kwalba wajen neman aikin da babu shi.