Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai bar Abuja yau zuwa Libreville, babban birnin ƙasa Gabon, domin ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Brice Clotaire Oligui Nguema.
A halin yanzu Shugaba Tinubu yana ziyara ta kwanaki biyu a Jihar Katsina.
A cewar Stanley Nkwocha, mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Kasa, Najeriya na goyon bayan sauyin mulki na dimokuraɗiyya cikin lumana a ƙasar Gabon kuma ta sake tabbatar da ƙudirinta na inganta dimokuraɗiyya a Afirka.
Oligui Nguema, wanda ya kasance shugaban riƙon ƙwarya na Gabon tun watan Agustan 2023, ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 12 ga Afrilu, inda ya samu kashi 94.85% na ƙuri’un da aka kaɗa.
- Rashin tsaro: ‘Ba za mu miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba’
- Yadda sojoji suka kashe manyan ’yan bindiga 5 a Zamfara
’Yan takara bakwai ne suka fafata, inda tsohon Firayim Minista Alain Claude Bilie-By-Nze ya zo na biyu da kashi 3%.
Ana sa ran Shettima zai dawo Najeriya bayan bikin rantsarwar.