Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya isa Kaduna domin ta’aziyyar rasuwar mutum sama da 90 a sakamakon harin jirgin soji kan mahalarta taron Mauludi a kauyen Tudun Biri a jihar.
Shettima ya kawo ziyarar ta’azizyar ce tare da Ministan Tsaro, Abubakar Badaru da kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Sauran ’yan tawagar sun hada da Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen, wanda dan Jihar Kaduna ne.
Akalla 87 da Kiristoci uku ne suka rasu, baya ga wasu mutum 66 ne suka ji rauni a harin bom din, wanda jirgin soji mara matuki ya kai a bisa kuskure a ranar Lahadi.
- Harin Mauludin Kaduna ba kuskure ba ne —Sheikh Gumi
- Gwamnan Sakkwato Zai Saya Wa Kansa Motocin Biliyan Daya
Tsautayin, wanda ya auku a yayin taron bikin Mauludi da wata makarantar Islamiyya ta shirya, wanda kuma ya samu baki daga wasu kauyuka makwabta.
Harin wanda Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta ba da hakuri a kai, ta ce tsautsayin ya auku ne a lokacin da take fatattakar ’yan ta’adda da suka addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
shi ne irinsa na 16 kuma mafi muni da jiragen sojin Najeriya suka yi kuskuren kaiwa fararen hula daga shekarar 2014 zuwa yanzu.
Akalla fararen hula 400 ne suka rasa rayukansu a hare-haren kuskuren da suka auku a yankin Arewacin kasar da ke fama da matsalar tsaro.