Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-rufa’i ya ce ba shi da sha’awar tsayawa takarar Shugaban Kasa a shekarar 2023 saboda shekarunsa ba za su iya jure dawainiyar aikin ba.
Mai kimanin shekaru 62 a duniya, Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da Sashen Hausa na BBC a ranar Asabar.
- Mulkin soja ake yi a Kaduna ba dimokuradiyya ba – Isa Ashiru
- ’Yan bindiga sun hallaka mutum 7 a Kaduna
El-Rufa’i, wanda bai kai ga kammala wa’adinsa na biyu a matsayin Gwamnan Kaduna ba ya ce tuni tsufa ya fara cimmasa.
Ya ce, “Mulkin Najeriya fa ba karamin al’amari bane, wanda bisa ga dukkan alamu yafi karfin mai shekaru 62 saboda tsufa.
“Kalle ni da kyau ka duba furfurata, idan ka ga hoto na lokacin da aka rantsar da ni gashin kaina baki ne, amma kalli yadda na koma yanzu.
“Wannan aiki ne mai matukar wahala, kuma wai Jiha daya nake jagoranta daga cikin 36, aikin ba karami ba ne, amma duk da haka ko kama kafar na Shugaban Kasa bai yi ba,” inji Gwamnan.
Da aka tambaye shi ko yana da sha’awar tsayawa takarar Mataimakin Shugaban Kasa sai ya ce, “Ko tunanin haka sam bana yi. Na sha nanatawa cewa a irin tsarin siyasar da muke kai, in Buhari ya kammala shekarunsa takwas, Kudu ya kamata a kai kujerar.