✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekaru 53 na ’yancin kai akwai gyara

Editan Aminiya ka ba ni dama in yi tsokaci kan ranar ’yancin kai. Hakika wadannan shekaru 53 na ’yancin kai ba mu da mahimmin ci…

Editan Aminiya ka ba ni dama in yi tsokaci kan ranar ’yancin kai. Hakika wadannan shekaru 53 na ’yancin kai ba mu da mahimmin ci gaban da ya wuce kasancewar Najeriya kasa guda, amma a har kokin inganta rayuwar talakawa mun ci baya. Matukar kasar nan za ta ci gaba, dole ne shugabanni su himmatu wajen shawo kan matsalar tsaro da kula da lafiya da ilimi. Kowa ya bayar da tasa gudunmuwar don inganta kasa. Daga Sanin Bola, Kano 08168555872

Sakonnin waya

Sojoji a daina karbar kudi

Assalamu alaikum, Aminiya. Don Allah ku gaya wa shugabannin Najeriya, su hana sojoji amsar kudi a hannun direbobi. Daga Abdul K.D. Tafa 07050985200

Addu’a ga Kwankwaso
Edita don Annabi Muhammadu (SAW) ka ba ni fili in yi addu’a da fatan alheri ga Gwamnan Kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso, saboda gyaran masallatan Juma’a guda 44 d ake Jihar Kano. Allah Yasa ya kamala mulkinsa lafiya duk na Annabi ya ce amin. Daga Ali Fancy  Garko A. Kano. 08171748500.

Ga ’yan kabu-kabun Gusau
Sallam. Aminiya, a yi mini kira ga ’yan kabu-kabun Gusau, kan lallai su bar ganganci. Nagode. Daga Idris Yaro 07061860202.

Manya a hana Kashe-kashe
Edita barka da aiki. Don Allah malamai da kuma manya Arewa da manyan jagororinmu. Ku rika sa baki a wannan kashe-kashe da ake yi ko Allah Zai sa a samu sauki. Manyan Najaeriya a yi hankali da taron da ake shirin shiryawa. Domin ’yan mjalisa ne ya kamata su yi, ba wasu daban ba. Daga Sani Abdu Beta 08095623376.

Ga Solomon Dalung
Assalamu alaikum. Edita don Allah ka ba ni dama na yi gaisuwa da jinjina ga Solomion Dalung a wannan jarida, mai farin jinni. Gaskiya Solomon Dalung wallahi kai namiji ne, kuma son al’ummar Najeriya. Daga Abdul Fresh Saminaka 08139333373.

Tumbin giwa
Edita da fatan za ku isar mani da gaisuwata ga Ado Sale Kankiya mai filin Tumbin giwa. Allah Ya saka da alheri a kan fadakar da jama’a abin da kasa take ciki da kake yi, ba tare da shakka ko tsoro ba. Daga Usman Mu’azu Funtua, Jihar Katsina 08106067660.

Ga Shatiman mawakan Bauchi
Gaba dai-gaba dai Shatiman mawakan Bauchi. Wallahi kowa  yabi fatan mu dai, Allah Ya kareka daga makiyanka. Daga Danso Fatara Azare Sit. 08138746876.

Mu tuna da matattunmu
’Yan Arewa muna lissafin ’yan uwanmu wadanda ba su ci ba, ba su sha ba ake ta kashewa ko domin wata rana mu tuna da su. Mu rika yi musu addu’a in ba mu yi haka ba, to kamar b amu damu da su ba. Daga Musa Adam Mile 12, Ketu Area, Legas. 08033811288.

Mu kiyayi gurbatattun al’adu
Aminiya ina son ku isar min da sakona ga ’yan uwa, don Allah mu daina kwaikwayon al’adun da ba su dace da mu ba. Daga H. Mamuda Kaddi, Dappon sojojin Najeriya.

Ga Gwamna Lamido na Jigawa
Salam. Aminiya amintacciyar jaridarmu. Ina so na yi amfani da wannan dama zuwa ga Gwmanan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido CON, ya taimaka wa sababbin daliban makarantar JICORAS ’yan Remedial da na IJMB, ta yadda za su samu shiga jami’a. Daga Yusuf Kasim Hadeja 07063427857.

Ga Nabila Ibrahim
Sallam. Aminiya don Allah ina so ku mika min sakon gaisuwata ga Nabila Ibrahim Khalil, Allah Ya ba ta ladar fadakar da ’yan uwa da take yi. Daga Farida H. Yakub R/Lemo 07036956980.

Ga danmajen Katsina
Salam Aminiya don Allah ina so ku ba ni dama in yi kira ga mai girma danmajen Katsina, wato Sanata Ibrahim Ida da ya amsa kiran da Katsinawa ke mashi, ya tsaya takarar Gwamnan Jiha, domin jama’a na cikin hali. Daga Mai kishin son ci gaban Jihar Katsina 07057828485.

Kwamiti ko yaudara?
Duk lokacin da aka samu wata hatsaniya ko asarar rayuka, ko gobara da sauran su, sai kaji gwamnati ta kafa kwamiti bincike, kamar da gaske! Amma abin takaicin shi ne da zarar ’yan kwamitin sun mika rahotonsu, ba za ka sake jin batun ba, sau nawa ana kafa kwamiti a kan batuuwa daban-daban, amma b amu taba jin an aiwatar da rahoton sakamakon binciken ba. Daga Nasiru Albani Bauchi. 08167155483.

Ga Masari
Aminiya ’yar amana, don Allah ku mika mana kira ga Dallatun Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari da ya kara amsa kiran talakawan Jihar Katsina, ya fito mana takarar Gwamna,a jam’iyyar Baba Buhari APC. Daga Musa Unguwar Mai Yasin danja, Jihar Katsina 08155648155.

Mu yi koyi da Buhari
Assalamu alaikum. Talakawa mu yi kokarin ganin Buhari ya yi wa kasar nan mulkin shekara hudu, don mu ga abin koyi a gare shi. Daga Yahaya A. Gurku Karu, Jihar Nasarawa 08180616523.

Ga jaridar Aminiya
Ban san har sau nawa ina yi muku sakon waya ba ku sanya shi a cikin jerin sakonninku. Da fatan sakon fatan alheri ga Bulama CIS zai samu shiga. Daga Abubakar M. batagarawa, Katsina 08087868555.

Dausayin kauna
Salam Edita don Allah a dawo da Dausayin kauna. Daga F.B. K. Fagge 08166914340

Ga wakilin Bichi a majalisa
Assalamu alaikum. Ina so a mika mana godiyarmu ga Hamza Sule Maifata dan majalisa mai wkailtar Bichi. Daga Ahmad Yola Bichi, Gidan Malamai 08088619667.

Ga mutanen Aljannare
Salam, Aminiya ga gaisuwata zuwa ga mutanen Aljannare, mazauna Legas. Daga Idris Yaro Abuja 07061860202.

’Yan mata a suturta kai
‘Yan mata a rika sanya sutura ta kamala, a kare tsiraici. Ku daina wulakanta kanku. Allah Ya yi muku sutura. Dag AbdulAzeez Maska Funtuwa 07068549745.

Ba mu yarda da taron kasa ba
Assalamu alaikum, Aminiya mu talakawan Najeriya ba mu yarda da taron kasa ba. Sai dai a yi ’yan majalisa, tsarin mulki ya ba dama. Daga dan-iya Trader kofar Wambai. 0704453447.