Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Tsakiya, kuma jagoran ‘yan bakwai da aka fi sani da (G7), ya zargi uwar jam’iyyar APC ta kasa da rashin adalci da nuna bambanci a tsakanin ‘ya’yanta.
Sanata Ibrahim Shekarau ya ce matakin da uwar jam’iyyar ta dauka na bayar da shaida tare da tabbatar da Abdullahi Abbas a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na Kano ranar Alhamis bai dace ba.
“Wannnan matakin babu adalci a cikinsa.
“Duk da mu mun fi wata biyu da hukuncin kotu a hannunmu, uwar jam’iyyar ba ta ba wa shugabannin bangarenmu shaidar tabbatar da shugabancin jam’iyyar ba,” inji shi.
- Matashi ya yi yunkurin kashe kansa saboda budurwarsa za ta auri wani
- Za a fara makala wa jami’an tsaro kyamara a jikinsu
Sanata Shekarau ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon murrya da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya kuma ce abin da uwar jam’iyyar ta yi ya nuna akwai wadanda aka dauka ‘yan mowa da ‘yan bora a cikin jam’iyyar, saboda yadda aka mika shaidar cin zabe ga bangaren Ganduje kasa da awa biyu da hukuncin Kotun Daukaka Kara.
Bugu da kari, Sanata Shekarau ya bukaci uwar jam’iyyar da ta yi kokarin yi wa kowa adalci saboda a samu daidaito kamar yadda ta ke ikirari a koda yaushe.
Sanata Shekarau, a madadin sauran magoya baya da masoya, ya bayyana cewa sun umarci lauyoyinsu da su daukaka kara bisa hukuncin na ranar Alhamis 17 ga watan Fabrairu 2022.
A daya bangaren kuma, Sanata Shekarau ya yi tir da abin da ya kira “kalamai na rashin arziki” da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya furta a kan ‘yan bangaren nasa bayan zartar da hukuncin kotu.
Idan za a iya tunawa Ganduje ya mayar da zazzafan martani ga bangaren Shekarau jim kadan bayan da Kotun Daukaka Kara ta rushe hukuncin da kotun baya ta yi.
Rahotanni sun ce bayan sanar da hukuncin an jiyo Gwamna Ganduje yana cewa “Banza Bakwai” sun fadi wanwar a kan rashin bin ka’idojin jam’iyya da amincewa da jagorancinsa.
“Abin da ‘yan Banza Bakwai suka yi kamar shuka dusa ne da damuna ko kuma ginin da aka yi fandisho da toka kuma a ce za a dora masa bulo”, inji Ganduje.
Gwamnan ya yi wannan magana ne a wani faifan bidiyo da ya nuna nuna shi yana jawabi ga wasu ‘yan majalisa da sauran mukarraban gwamnatinsa.
Idan ba a manta ba rikicin shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano, ya samo asali ne lokacin da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya gudanar da na shi zaben, shi ma Sanata Ibrahim Shekarau ya gudanar da na shi zaben.
Tsagin gwamna Ganduje sun zabi Abdullahi Abbas a matsayin wanda zai ci gaba da shugabancin jam’iyyar APC a jihar.
Kazalika, tsagin Sanata Shekarau sun zabi Haruna Zago a matsayin wanda zai karbi ragamar shugabancin jam’iyyar.
Sai dai zaben ya bar baya da kura, ‘ya’yan jam’iyyar suka rabu gida biyu, wato tsagin gwamna Ganduje da tsagin Sanata Shekarau.
Lamarin da ya kai ga zuwa kotu, inda tsagin Sanata Shekarau ya fara yin nasara a kotu, kafin daga bisani kotun daukaka kara ta warware hukuncin kotun, tare da bai wa tsagin gwamna Ganduje nasara.
Tuni shugabancin jami’iyyar APC na kasa ya gabatar da takardar shaida ga Abdullahi Abbas, a matsayin shugaban jam’iyyar APC na Kano.