✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara daya da kisan manoma 48 a Zabarmari

An yi juyayin tunawa da kisan da aka yi wa manoman shinkafa a Zabarmari shekara guda da ta gabata.

Shekara guda ke nan da kai wa wasu manoma hari a garin Zambarmari da ke Karamar Hukumar Jeren Jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya.

A ranar Lahadi ce mazauna garin Zabarmari suka yi juyayin tunawa da kisan kiyashin da aka yi wa wasu manoman shinkafa a gona shekara guda da ta gabata.

Al’ummar garin Zambarmari sun gudanar da addu’o’i da juyayin tunawa da kisan da mayakan Boko Haram suka yi wa manoman shinkafa 48 a ranar 28 ga watan Nuwambar 2020.

Wannan kisan kiyashi da aka yi wa al’ummar Zabarmari wanda kungiyar Boko Haram ta dauki alhaki ya gudana ne a garin Koshebe da ke makwabtaka da Karamar Hukumar Mafa a Jihar Borno.

Bayanai sun ce lamarin ya gudane ne yayin da manoman Zabarmari ke gonakinsu a wurare daban-daban da suka hada Zabarmari, Koshebe, Balaburin, Karkur, Gudda, Gudda Cizama da Azaya, inda mayakan suka tattara su a Koshebe suka yi musu yankan rago.

Sakateren Kungiyar Dillalan Shinkafa a Jere, Malam Mikail Mohammed, ya ce mutane ciki har da sarakunan gargajiya sun taru inda suka gudanar da adduoi da rokon Allah Ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya da kuma adduoin wanzar da aminci da tsare musu rayuka da dukiyoyi.

A cewarsa, har yanzu wasu daga cikin iyalan manoman da aka kashe suna fuskantar matsi na rayuwa wanda ko shakka babu suna bukatar agaji.

Ya ce dukkan mutanen da aka kashe a waccan rana, al’ummar garin Zabarmari ne wanda shi ne yankin da ya fi ko’ina noman shinkafa a duk fadin Jihar Borno.

Ya ce aukuwar lamarin ya firgita manoma, wanda galibi suka bar amfanin gonakinsu kwari da tsuntsaye su cinye.

Sai dai ya ce daga bisani an turo sojoji yankin wadanda suka rika rakiyar manoman zuwa gonakinsu duk rana a kullum har zuwa lokacin da suka yi girbi.

Ya ce wannan taimako da manoman suka samu ya taka rawar gani gaya duk da cewa akwai wadanda ba su koma gonakinsu ba sai a bana.

Mika’ilu ya ce a bana dai ba a samu albarkar noma ba, lamarin da ya alakanta da karancin saukar ruwan sama, sai dai ya ce sun fara shirin noman rana wanda kuma suna sa ran za a samu biyan bukata.

Ya ce galibin al’ummar kauyen sun koma gonakinsu a bana wanda a bara aka bari fayau amma a yanzu cike suke da yabanya ta shinkafa.

“Mafi akasarin gonakin da ba a yi shuka ba suna da nisa sosai da hakan ya sa manoma ke fargabar zuwa. Amma a halin yanzu, mutane sun koma gonakinsu inda suka yi shukar shinkafa da wasu hatsin irinsu waken-suya da masara” a cewarsa.

Mika’ilu ya yi kira ga hukumomi da su taimaka wa kananan manoma da kayan noma domin bunkasa harkokinsu a yayin da matsalar ta’addanci ke ci gaba da ja baya.

 Wani manomi daga garin Koshebe, ya ce har yanzu mutane na fama da radadin kashe manoman da aka yi da kuma halin kaka-nika-yi da iyalan wadanda aka kashen suke ciki.

A cewarsa duk da cewa ba a sake samun aukuwar makamancin wancan hari ba, amma har yanzu akwai kananan hare-hare da ake aukuwa, lamarin da ke hana manoma fita gonakinsu.

Ya yi kira ga mahukunta da su samar da hanyoyi masu kyau ga alummar karkara a yankunan.

Zulum ya bayyana takaicinsa

Gwamna Babagana Umar Zulum wanda ya jagoranci jana’izar mamatan a bara, ya bayyana harin a matsayin abin takaici tare da jajanta wa al’ummar yankin da cewa gwamnati za ta yi iyaka kokarinta don ganin an shawo kan wannan lamari.

Kari a kan jamian tsaro da gwamnatin tarayya ta jibge a Jihar Borno, daga bisani Gwamna Zulum ya dauki mafaruta 1,000 domin samar da tsaro ga manoma da mazauna yankunan karkara.

 Tun a wancan lokaci, iyalan manoman da ka kashe yayin harin sun samu tallafi na kudi da kayayyakin abinci.

Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Borno, Saina Buba, ya ce an ba kowane daya daga cikin iyalai 48 na ’yan uwan wadanda aka kashe tallafin Naira dubu dari shida-shida da kuma buhunan kayyayakin abinci a karkashin sa-ido da jagorancin kwamitin rabon kayan tallafi da Gwamna Zulum ya kafa.

Ya ce an samu kudaden ne daga tallafin hadin gwiwa na Naira miliyan 20 da Kungiyar Gwamnonin Arewa na Najeriya da kuma tallafin Naira miliyan biyar da Hukumar Raya Arewa maso Gabas (NEDC) ta bayar.

Dangane da kayyayakin abinci da aka raba, Kwamishinan ya ce buhuna 13,000 na shinkafa, masara da wake da kuma jarkokin man gyade 1,300 da katan-katan 2,116 na sunadarin dandano, da kuma tumatur da gishirin leda 1,733 Ma’aikatar Kula da Ayyukan Jinkai, Agaji da Bunkasa Walwalar Al’umma ce ta dauki nauyi.

Domin sake karfafa gwiwar manoma, dan Majalisa mai wakiltar Jere a Tarayya, Honarabul Satomi Ahmed, ya bayar da tallafin injinan sarrafa shinkafa guda 250 a yankin Zabarmari domin manoma su ci moyarsu yayin noman rani a bana.

Ana iya tuna cewa, a hannu guda kuma, wata sanarwa da ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da bayar da agaji ya fitar, ya nunar da cewa sama da mutane 100 ne ’yan ta’addan suka halaka.

Sanarwar ta bayyana kisan da mafi muni a bara, inda ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta tabbabar an hukunta wadanda su ka yi wannan aika-aika.