Kungiyar Dalibai Musulumi ta Najeriya (MSSN) ta cika shekara 68 bayan an kafa ta a ranar 18 ga watan Afrilun 1954.
An kafa kungiyar ce da nufin hada kan dalibai Musulmi ba tare da la’akari da bambancin akida ko sauran bambance-bambance ba.
- Duk da tubar dubban ’yan ta’adda a dage da addu’o’i —Zulum
- Ministan Kwadago ya fito takarar shugaban kasa
A sakonsa na taya kungiyar murnar cika shekara 68, Shugaban Kungiyar ’Yan Jarida Musulmi ta Najeriya (MMPN), Abdur-Rahman Balogun, ya ce “Nasarorin da MSSN ta yi a baya sun samu ne saboda sadaukar da kai da jajircewa da manufar da aka sa a gaba duk kuwa da matsalolin da ta fuskanta a shekarun baya.”
Ya kara cewa a tsawon tarihin kungiyar ta horar da mambobinta bisa koyarwar Musulunci, domin samun hadin kan kasa da kuma ci gabanta, sabanin yadda kungiyar take gudanar da harkokinta a yanzu.
A cewarsa an kafa kungiyar MSSN ne daidai da ayar da yi kira ga Musulmi su yi riko da igiyar Allah, su hada kai, kada su rarrabu.
Ya bayyana cewa saboda da hadin kan da kungiyar take da shi a lokacin, MSSN ta samar da kwararrun manajoji, gwamnoni, ’yan majalisar dokoki, shugabannin jami’a, shugabannin ma’aikatun gwamnati da ministoci da sauransu.
Sai dai ya koka da cewa duk da yawan mambobin kungiyar MSSN daga baya an samu yaduwar wasu kananan kungiyoyi da akidu saboda son zuciya.
Hakan ne a cewarsa, da ya kawo matsala ga gishikin da aka kafa kungiyar na samar da hadin kai da kaunar juna a tsakanin dalibai Musulmi.