✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 61 na mulkin kai: Me za a yi wa murna?

A shekara 61 na mulkin kan Najeriya gaba aka yi ko baya?

A makon jiya ne aka yi bikin cikar Najeriya shekara 61 da samun mulkin kai daga hannun Turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

An yi shagulgala da jawabai a tsakanin gwamnoni da fadar Shugaban Kasa, an shirya kasaitaccen biki a Abuja, fadar Gwamnatin Tarayya, inda aka yi wasanni iri-iri duk da nufin murnar wannan rana ta samun ’yanci ko mulkin kai.

Shugaban Kasa da mukarrabansa da suka kunshi ministoci da manyan hafsoshin tsaron kasa da dukkan wadansu kusoshin gwamnati sun taru a Dandalin Eagle Square, inda aka yi ta nishadi da wasanni domin bikin wannan rana.

Haka nan abin yake a jihohi, inda da yawan gwamnonin jihohin Najeriya, suka karbi faretin ban-girma a filayen wasanni da manyan wuraren tarurruka a jihohinsu don bukukuwan cikar Najeriya shekara 61 da samun mulkin kai.

A daidai lokacin, daliban makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya da ke Yawuri a Jihar Kebbi sun shafe fiye da kwana 100 a hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

Kuma a daidai lokacin da darururuwan mutane suke hannun masu garkuwa da su a dazukan Kaduna zuwa Abuja da hanyar Funtuwa zuwa Gusau zuwa Lambar Tureta zuwa Sakkwato.

Haka a Katsina da Neja da sauran garuruwan Najeriya, an kama mutane an yi garkuwa da su.

A irin wannan yanayi Shugaban Kasa da Gwamnoni suke tsaye ana kade-kade da bushe-bushe da wake-wake wai da sunan murnar samun mulkin kai?

Abin tsoron shi ne, yadda lamarin satar mutane da yin garkuwa da su ya zama ba sabon labari ba.

Abin ya zama ba wani abin ta da hankalin hukumomi ba, tashin hankalin bai wuce na dangin da aka sace musu dan uwa ba, su ne kawai suke cikin zullumi da damuwar rashin ganin dan uwansu.

Amma a bangaren hukumomi wannan ba tashin hankali ba ne, kuma ba wata damuwa ba ce da za ta hana yin shagulgulan duk da halin da al’ummar kasa take ciki.

A farkon zuwan Shugaban Kasa, ya ce ba zai yi irin wadannan bukukuwa ba saboda halin da kasa take ciki na tsaro, musamman a jihohin Borno da Yobe.

Shin yanzu da Shugaban Kasa ya halarci wadannan bukukuwa an samu sauyi ne na halin da al’ummar kasa suke ciki na daga tsanani zuwa walwala da rashin tsaro zuwa aminci daga yunwa da fatara zuwa karuwar arziki da walwala?

Shin an samu sauyi ne na halin da ake ciki daga Jibiya zuwa Borgu ko daga Kwangwalam zuwa Sabon Birni ko daga Baga zuwa Yawuri?

Nuna halin ko-in-kula a kan batun tsaro da zaman lafiyar al’umma shi ne yake kara ta’azzara lamura a Najeriya.

Yanzu dai za mu iya cewar dimokuradiyya na samun ci gaba a Najeriya, yadda ake bukukuwan mulkin kai da ranar dimokuradiyya da sauran bukukuwan da hukumomi suke jagoranta da sunan dimokuradiyya.

Daga 1999 zuwa yanzu irin arzikin da Najeriya ta samu Allah ne kadai Ya san adadinsa, an yi facaka, an yi wadaka, an yi duk abin da za a iya, wanda ido zai iya gani da wanda ba zai iya gani ba, na barna da ta’adi da dukiyar kasar nan, maimakon talakawa su samu sassauci da irin dimbin arzikin da Allah Ya hore mana, sai dai karin kunci da wahala da shiga halin ha’ula’i.

Daga dawowar wannan dimokuradiyya ta 1999 zuwa yanzu mene ne farashinsa yake nan bai canja ba? Mene ne abin da farashinsa ya yi kasa daga yadda yake?

Shin daga 1999 zuwa yanzu karuwar arziki aka samu ko koma-baya ta fannin tattalin arziki?

Babu wani dan Najeriya da ya kwana ya tashi da yake bukatar a gaya masa, ko a ba shi labarin halin da ake ciki a Najeriya na wahala da al’ummar kasa ke sha da kuma gazawar hukumomi da ake samu.

Idan ka dubi unguwannin masu hannu da shuni da tituna, za ka ga an samu sauyi, ga manyan gidaje nan na alfarma an gina, ga tituna ga manyan motoci na kece-raini suna kai-komo a tituna, masu mulki da mukarrabansu da matansu da ’ya’yansu ga su nan suna sanya suturu masu dan karen tsada suna kece-raini a wuraren bukukuwa, dukiya kam a tsakaninsu ba a magana, kai ka ce babu wata matsala da ake fama da ita a Najeriya.

Amma idan za a yi duba na tsakani da Allah, harkar ilimi a kasar nan karuwa ta yi ko ci baya? An samu karuwa ta yawan makarantu da yawan dalibai da yawan malamai kam.

Amma ingancin ilimi ya sake komawa baya, maimakon a samu kwararrun dalibai da malamai, sai kullum abin yake sake komawa baya.

Malamai sun zama kwashi-kwaraf, babu basira, babu hangen nesa babu tunani. Yara sun zama wani abu daban.

Ilimi kadai idan ka dauka ka zazzage shi sai ka ce to wai ta ina aka samu ci gaba a kasar nan?

Ban da sauran fannonin rayuwa da kullum ake nan jiya-i-yau, harkar lafiya ta lalace, jami’an gwamnati da masu kudi da masu karamin karfi kowa ya gwammace ya je Indiya ko Masar ko Dubai neman lafiya.

Jami’an gwamnati da masu iko sun daina gamsuwa da likitocin kasar nan, sun koma zuwa Ingila da Amurka su da matansu da iyalansu, an bar talakawa da kwashi-kwaraf.

Haka nan harkar sufuri ta lalace, masu mulki sun koma amfani da jiragen sama.

Ba sa bin hanyoyin mota su yi tafiyar kilomita 200 ko 300, balle su san halin da ake ciki a kan hanyoyin.

Tunda Shugaban Kasa ya hau mulki bai taba yin tafiyar da ta kai nisan kilomita 100 a kan hanyar mota ba, kuma bai taba kai ziyarar ba-zata inda ake aikin hanyoyi ba!

Shi sai dai a je fadar gwamnati a yi masa bayanin ga halin da ake ciki, shin anya mulki zai yiwu da haka?

Amana ce aka dora a wuyan Shugaban Kasa, amma yana sakaci ya dora wadansu mutane kuma ba ya bibiyar aikin da ya ba su ta hanyar ziyarar ba-zata don gani da idonsa.

Kullum sai bayani na cewa ana sane da halin da al’umma suke ciki na tsanani da wahala. Ta yaya ake sane?

Shugaban Kasa bai taba kai ziyarar ba-zata wani kauye ya ji halin da talakawa suke ciki ba, idan ma ya je wata jiha sai dai ya zauna a gidan gwamnati a kirawo wadansu mutane a tsara musu abin da ake son su gaya masa wanda yake son ji.

Allah Ya jikan Shugaban Jamhuriyyar Nijar ba don ya mutu ba, mun ga yadda Shugaba Bazoum yake shiga kauyuka masu nisa yana ganin halin da al’umma suke ciki, yana magana da su kai-tsaye ba tare da an tsara  wadanda za su yi masa magana ba, shi da kansa yake zaben wanda zai yi magana don jin kokensu.

A irin wannan hali da ake ciki murnar me za a yi? Mawuyacin halin da al’ummar kasa suke ciki, ko kuwa halin walwala da facaka da masu mulki suke ciki?

Ba mu da wata kasa sama da Najeriya, burinmu da fatarmu su ne ta ci gaba.

Shugabanninmu ba mu da wata kiyayya a kansu, burinmu shi ne su canja su mayar da hankali ga ci gaban al’umma ba ci gaban kawunansu da iyalansu ba.

Yasir Ramadan Gwale

([email protected]) 08023917104 (Tes kawai).