Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada sharadin dage takunkumin da aka sanya wa Kamfanin sadarwa na Twitter a Najeriya.
Cikin jawaban da ya gabatar ga ‘yan Najeriya na cikar kasar shekaru 61 da samun yancin kai a ranar Juma’a, Buhari ya ce dole sai Twitter ya cika sharudan da gwamnatinsa ta gindaya gabanin janye takunkumin da aka sanya masa.
- Najeriya A Yau: Shekara 61 Da Mulkin Kai: Gaba Najeriya Take Yi Ko Baya?.
- Mayakan ISWAP jirgin soji ya kashe a Borno ba masunta ba
Tun a ranar 5 ga watan Yunin da ya gabata ne Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shafin Twitter kan abin da ta yi zargin cewa, ana amfani da dandalin sada zumuntar wajen wargaza hadin kan al’ummar kasar.
Shugaba Buhari ya ce an dauki matakin hakan ne don ba wa gwamnati damar daukar matakan da suka dace na tace ire-iren bayanan da ake yadawa a shafin.
Buhari ya ce gwamnatinsa ta nada kwamitin da zai zauna a teburin sulhu da wakilan Twitter domin warware sabanin da ya kai ga an dakatar da amfani da shafin a Najeriya.
“Biyo bayan dakatar da shafin Twitter ne mahukuntansa suka tuntubi gwamnatin Najeriya don yin sulhu. Kuma na kafa kwamitin da za su zauna don warware matsalar da ta janyo muka dauki mataki.
“Kwamitin sun zauna da wakilan Twitter kuma sun tattauna dangane da abin da ya shafi sha’anin tsaro a kasar nan wajen wallafa abubuwa a shafin.
“Bayan shafe lokaci ana tattaunawa, na ba da umarnin a dage dakatarwar da aka yi wa shafin in har an cika sharudan da aka kafa musu, don bawa ‘yan kasa damar yin kasuwanci da sauran harkokinsu a shafin.”
Shugaba Buhari, ya zayyana abubuwa da dama da Najeriya ta samu na ci gaba tsawon shekara 61 da kafuwarta a matsayin kasa tun bayan samun ‘yancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka.