Jawabin shugaban kasa na Bikin Zagayowar Ranar Samun Mulkin Kai a wannan karon ya bambanta da na baya, saboda akwai tuna baya a cikinsa.
Ya bude jawabin ne da matsalolin da kasa ke fuskanta, tare da jaddada kalubalen da ta samu kanta a ciki na yankin basasa; da mulkin soja na tsawon lokaci; da karuwar al’umma; da matsalar tattalin arzikin kasa; da matsalolin tsaro; da tabarbarewar aikin gwamnati; da kirkirar matsalolin son rai (amma a sa su zamto kamar daga Allah, ko tsautayi, ko game duniya da ba za iya kauce musu ba).
- Bikin Shekara 60: Mun Fi Daukaka A Dunkule —Buhari
- Bai Dace Najeriya Ta Fi Saudiyya Arahar Man Fetur Ba —Buhari
Jawabin ya bambanta saboda ba a tuna baya kadai ya tsaya ba, ya ja hankali a kan a hadu a bayar da gudummawa domin ganin an gina kasa daya TARE.
An yi ta nanata a hada kai.
Ya kuma mayar da hankali kan tsare dokokin kasa, sannan ya yi alfahari da kara sahihancin zabe, inda ya ba da misali da zaben Jihar Edo.
Ya kuma dubi rashin gaskiya da ya yi katutu a bangaren shari’a da barazanar hakan.
Jawabin ya kuma dan ba da haske a kan dogon burin kasar na zama daya daga cikin kasashen duniya 20 masu karfin tattalin arzikin, da kuma fitar da ’yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekara 10.
Karshen jawabin ya mayar da hankali ne a kan hanyoyin da gwamnati ta kirkira na yakar rashin aikin yi da talauci, da kokarin kare kai ko fahimtar da mutane kan karin man fetur, ta hanyar daganta farashin shi a Najeriya da sauran kasashe.
Kabiru Sufi Sa’id malami ne a Kwlaejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (CAS) kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum.
Fassara: Hamizu Kabir Matazu