✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 53 da samun ’yancin kai

A ranar Litinin da ta gabata Najeriya ta cika shekara 53 da samun ’yancin kai bayan mulkin Turawan mulkin-mallaka. A lokutan baya idan aka ce…

A ranar Litinin da ta gabata Najeriya ta cika shekara 53 da samun ’yancin kai bayan mulkin Turawan mulkin-mallaka. A lokutan baya idan aka ce ranar samun ’yancin kai ta zagayo za a rika murna da farin ciki, amma a yanzu wannan ya zama tarihi wanda ya samu nasaba da matsalolin da suka yi cacukwi da kasar. Akwai abubuwan tunawa da ke kunshe da takaici. An  kuma yi hasarar damammaki a yanzu kuma gwiwa ta sanyaya.
Duk da alamun da ke nuna bunkasa tattalin arziki amma bai yi tasiri a mafi yawan bangarorin al’umma kasar nan ba, don haka a irin wannan rana ta samun ‘yancin kai ya kamata a rika yin bayanin ci gaban da aka samu.
A lokacin da aka samu ’yancin kai ‘yan kasa sun yi fatan samun gwaggwabar rayuwa. A lokacin ba a samun man fetur ba, an dogara a kan noma ne kuma tattalin arzikin kasa ya bunkasa. A yanzu da muka shekara 53 muna mulkin kanmu sai muka dogara a kan kudaden shigar da muke samu daga man fetur wanda ya sanya al’amura suka lalace, komai ya tabarbare saboda rashin zuba hannun jari da kuma dabi’ar kula da kayayyaki. A makon jiya aka kai hari Kwalejin Koyar da Aikin Noma a Jihar Yobe har aka kashe dalibai kusan 70, wannan ya nuna batun matsalar tsaro akwai sauran rina a kaba, ba kamar yadda jami’an tsaro suke cewa sun ci nasara a kan masu tayar da kayar bayan ba.
Masana a kan tattalin arzika daga kasashen duniya da kuma Najeriya sun ta’allaka koma bayan tattalin arzikin kasar a kan cin hanci-da-rashawa da rashin kwararan matakan bunkasa tattalin arziki da aikata manyan laifuffuka da kuma son zuciya. Ba kawai a Najeriya ake da matsalar cin hanci da rashawa da aikata sauran laifuffuka ba, amma me ya sa sauran kasashe masu fama irin matsalolinta tattalin arzikinsu ya fi na Najeriya bunkasa? Za a iya cewa matsalar shugabanci ce.
Abin mamaki da takaicin shi ne kasar nan ta mallaki albarkatun kasa da na mutane wadanda ba a yi amfani da su yadda suka dace ba, shi ya sa aka kasa bunkasa tattalin arzikin kasar yadda ya dace.
A lokacin zaman majalisar dattawa kan dacewa ko rashin dacewar a taya Najeriya murna samun ‘yancin kai, sanatoci sun nuna takaicinsu wajen rashin samun ci gaban a-zo-a-gani musamman idan aka kwatantata da takwarorinta irinsu Brazil da Malaysia.
A yanzu ga batun tattaunawa a kan makomar kasa da ya bijiro, wannan batun ba zai haifar wa kasar nan da mai idanu ba. Wannan taron zai kara kambama kabilanci da bambancin addini da yare da addini da sauransu wanda maimakon a samu zaman lafiya sai dai a kara farraka kan jama’a.  ‘Yan siyasa su ne ummul’aba’isin wannan matsala ta rashin hadin kan ’yan kasa, domin su ne a lokacin kamfen suke zuga mutanensu hade da nuna musu bambancin addini da yare da bangaranci da sauransu.  Hanya daya ta magance hakan ita ce ‘yan siyasa su daina gwara kan mutane don su cim ma burinsu na siyasa, idan ba haka ba kuwa mun yi hannun-riga da hadin kai a kasar nan.
Akwai abubuwan yaba wa kasar nan tun bayan samun ‘yancin kai, domin kasar nan ta taka muhimmiyar rawa wurin samar da hadin kai a Nahiyar Afrika, misali yadda ta yi ruwa da tsaki wajen kawo karshen rikicin kasar Angola wanda a yanzu ana alfahari da hakan. Sojoji da ‘yan sandan Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen kwantar da tarzoma a kasashen duniya masu fama da rikice-rikice an kuma yaba musu kan hakan, idan haka ne yaya aka yi matsalar tsaro ta gagare su a Najeriya? Ya kamata a samar musu da kayan aikin da za su kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.
Ko masu rike da madafun iko a kasar nan sun yarda an gaza a yawancin fannoni. A halin yanzu ana bukatar shugabanni nagari, zakakurai masu kuma adalci don ceto Najeriya daga halin da take ciki.
Hanyar fita daga halin kunci da kasar nan take ciki ita ce a samu gwamnati mai adalci, a kuma ba kowane bangare damar gudanar da ayyukansa yadda suka dace, a kuma tabbatar da tsaro.