A ranar Juma’a ce aka cika shekara 34 da kisan fitaccen dan kishin Afirkan nan kuma tsohon Shugaban Kasar Burkina Faso Kyaftin Thomas Sankara, kisan da ya kada hantar mutanen Afirka a wancan lokaci.
Yanzu haka mutum 14 wadanda ake zarginsu da hannu a kisan mutumin da aka fi sani da Che Guebaran Afirka, suna fuskantar shari’a kan wannan kisa.
- Miji ya kashe matarsa a kan dumame
- ‘Yadda tsoffin janar-janar suke juya siyasar Najeriya ta bayan fage’
Sojoji ne suka harbe marigayin Shugaban mai matukar kwarjini a lokacin da yake da shekara 37 a duniya, a wani juyin mulki ranar 15 ga Oktoban 1987, lamarin da ya sa babban abokinsa Blaise Compaore ya maye gurbinsa.
Shekara hudu kafin nan, Compaore ne ya tsara gudanar da lamarin da ya zama silar zaman Sankara Shugaban Kasa, kamar yadda BBC ya ruwaito.
Mista Compaore yana daga cikin mutum 14 da ake zargi da hannu a kisan kuma a yanzu haka yana zaman gudun hijira a kasar Ivory Coast mai makwabtaka, inda ya tsere bayan tursasa shi yin murabus daga mulki a wata gagarumar zanga-zanga da aka yi ta yi a shekarar 2014.
Sai da ya sha musanta cewa yana da hannu a kisan Sankara kuma ya yi ta guje wa zaman sauraron karar.
Duk da shudewar lokaci, Sankara ya ci gaba da zama abin girmamawa a Afirka – ana yawan lika hotunansa a jikin motocin tasi-tasi a fadin Afirka ta Yamma, yayin da a Afirka ta Kudu kuma, babban dan hamayyar nan Julius Malema yake bayyana shi a matsayin abin koyinsa.
Sakataren Kwamitin Tunawa da Thomas Sankara, Mista Luc Dimaba ya bayyana dalilin da ake yi wa Sankara kallon gwarzo da cewa, “Muna kallon Sankara a matsayin mai kishin kasa.
“Ya kaunaci mutanensa. Ya so Afirka. Ya sadaukar da rayuwarsa saboda mu.
“A karkashin mulkinsa ne aka sauya wa kasar suna – daga Upper Bolta zuwa Burkina Faso, wato “Kasar Mutane Masu Gaskiya.”
Sankara ya yi rayuwar tsantseni. Ya rage yawan albashinsa da na sauran ma’aikatan gwamnati.
Ya kuma haramta amfani da direbobin gwamnati da sayen tikitin babbar kujera a jirgin sama.
Ilimi shi ne babban abin da ya bai wa muhimmanci, yawan masu ilimi ya karu daga kashi 13 cikin 100 a 1983 zuwa kashi 73 cikin 100 a 1987, ya kuma jagoranci gagarumin wayar da kai kan riga-kafi a kasar.
Sannan ya kwace gonaki daga hamshakan masu kudi ya mika wa manoma talakawa, abin da ya jawo bunkasa a fannin sarrafa alkama.
Sankara ya yi kira ga hadin kan Afirka don nuna adawa da abin da ya kira sabon mulkin mallaka na hukumomi kamar su Asusun Lamuni na Duniya da Bankin Duniya.
An taba ambato shi yana cewa: “Duk wanda ya ciyar da kai, zai juya akalarka.”
Ya ari wani tsarin manufofin kasashen waje da ke kalubalantar mamayar Faransa, da ya samu karfin fada-a-ji a kasashen da ta yi wa mulkin mallaka a Afirka, kamar su Burkina Faso.
Matarsa Mariam ta zargi Faransa da kitsa kisansa.
“Har gobe shi ne Shugaban Kasata. Abin da ya yi wa matasa ya ba mu kwarin gwiwa na yin koyi da shi,” kamar yadda wani dalibin Jami’ar Thomas Sankara a Ouagadougou ya shaida wa BBC.
A shekarar 2019 aka kaddamar da wani mutum-mutumi na tagulla mai tsawon mita shida a Dandalin Tunawa da Thomas Sankara da ke tsakiyar babban birnin kasar Ouagadougou, sannan a 2020 aka sake gyara shi bayan samun korafe-korafe a kan na farkon.
Mista Damiba ya ce ana shirin fadada dandalin, da ya hada da gina wata babbar husumiya da za a rika ganinta daga ko ina a fadin Ouagadougou.
Sannan za a gina wa Sankara wani hubbare da sinima da laburare duk da sunansa.
Ana sa ran wadannan gine-gine za su aika sakonnin muradin juyin-juya halin Sankara ga al’umma ta gaba.
Masu sukarsa fa?
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun sha sukar tsare-tsaren Sankara na neman kawo sauyi.
Wani rahoto da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta sake a 1986 ya bankado cewa an kama ’yan hamayyar siyasa an tsare su ba tare da gurfanar da su a gaban kotu ba sannan aka azabtar da su.
Serge Theophile Balima wanda ya rike mukamin Minsitan Yada Labarai a mulkin Sankara ya ce: “Ina gaya masa ya rika yin tafiyar hawainiya wajen yarda da batun dimokuradiyya mai jam’iyyu da dama kuma masu hamayya da shi ba sa iya yi masa magana kuma ba a sauraronsu.”
Me ya sa ake ta jan shari’ar kisansa?
Dan uwansa, Paul Sankara ya ce: “Mun dade muna jira tsawon shekara 27 na mulkin Blaise Compaore.
A lokacin mulkinsa ba mu ma taba koda mafarkin yiwuwar yin shari’ar ba.”
Matarsa ta shigar da korafi a 1997 kan kisan mijinta, amma an shafe shekara 15 kafin Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa za a ci gaba da bincike.
Kazalika, ba a samu wani ci gaba sosai ba, har sai bayan kifar da gwamnatin Mista Compaore a 2014.
Shekarar da ta biyo baya an gudanar da gwajin kwayoyin halitta na DNA a wata gawa da aka tono wacce aka yi zaton tasa ce, amma bayanan gwajin ba su iya tabbatar da hakan ba.
A 2016, hukumomin Burkina Faso sun nemi gwamnatin Faransa ta saki bayanan soji a kan kisan Sankara.
An karkasa wadannan bayanan aka rika aika su Burkina Faso bi-da-bi – na karshen shi ne wanda aka aika a watan Afrilun bana.
Wadanda ake tuhuma da kisan Ana sa ran za a tuhumi tsohon Shugaban Ma’aikatan Compaore, Mista Gilbert Diendere da wadansu mutum 11 a kotun soji “kan kai hari kan tsaron kasa,” da “kitsa kisan kai” da boye gawarwaki.
Tuni aka kai Diendere gidan yari, bayan yanke masa hukuncin daurin shekara 20 kan rawar da ya taka a juyin mulkin 2015 da bai yi nasara ba.
Daga cikin wadanda ake zargi har da Diebre Jean Christophe, likitan da ya sa hannu kan takardar tabbatar da mutuwar, inda ya ce tsohon Shugaban Kasar ya yi mutuwar Allah da Annabi ne ba kashe shi aka yi ba, Ana tuhumarsa da sauya bayanai.
Daya mutumin da ake tuhuma Hyacinthe Kafando ba ya nan, kuma shi ne tsohon babban mai tsaron Misa Compaore, wanda aka sa cigiyarsa a kasashen duniya da ba da umarnin kamo shi.
Ana zarginsa da jagorantar tawagar da ta kashe Sankara da wadansu mutum 12.