✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shekara 31 da samun ’yanci: Yadda yakin Rasha ya raba kan ’yan Ukraine

Ukraine na bikin cika shekara 31 da ficewa daga Tarayyar Soviet a 1991

Kasar Ukraine na ci gaba da gudanar da bikin ciki shekara 31 da ficewa daga Tarayyar Soviet a shekarar 1991.

To sai dai rahotanni na ni da cewa ana ci gaba da samun rarrabuwar kai tsakanin jiga-jigai da sauran ’yan kasar musamman kan yakinta da Rashan.

Ko a watan Yulin da ya gabata, sai da shugaban kasar, Volodymyr Zelenskyy ya tube wasu manyan jami’an tsaron kasar, bisa zargin su da cin amanar kasa.

Wadanda aka aka sallama sun hada da shugaban sashin tsaro na SBU, wanda aminin Zelenskyy ne tun yarinta, da jagorar ’yan sanda masu gabatar da kara, Iryna Venediktova — lamarin da ya jawo hankalin al’ummar duniya sosai.

Har wa yau a watan na Yulin, Zelenskyy ya yi makamncin wannan zargi kan wasu jami’an kasar 650, inda ya ce 60 daga cikinsu na yi wa Rashan aiki ne a yankunan Ukraine din da ta samu galaba.

Kafar yada labarai ta AFP dai ta rawaito cewa a baya-bayan nan akwai akalla manyan jami’an tsaron Ukraine uku da ke tsare a kurkuku, sakamakom zargin su da cin amanar kasa.

Rabuwar kai tsakanin ’yan Ukraine

Sai dai ko a cikin kasar ma wannan batu ya samu karbuwa da mabambambtan ra’ayoyi.

Wata lauya mai fafutuka a Cibiyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da ke Kyiv, babban birnin kasar, Tetiana Shevchuk,  a wata hirarta da Aljazeera ta ce sam hakan bai dace ba.

“Ba yunkuri ba ne da aka yi don ya dace. Wani yunkuri ne na samun karin iko a kan manyan hukumominmu na tilasta bin doka,” in ji ta.

Shi ma wani dattijo a kasar, Vladimir Shaverin, ya ce duk da yana fatan Ukraine ta samu nasara a yakin ta da Rasha, ya fi fatan al’umma za su daina kallon waye ya fito daga Ukraine ko Rasha.

“Bayan haka, idan muka samu nasara a yakin nan, dole ne gwamnati da al’ummar Ukraine su sauya, dole a kawo karshen cin hanci da rashawa in dai ana son samun cigaba mai dorewa”, in ji shi.

Duk da al’ummar kasar da dama na bayyana farin cikinsu da wannan rana, yawancinsu a Kyiv sun kasance a gidajensu, bisa fargabar hari daga Rasha.