✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shekara 10 da kisan Ghaddafi : Gara jiya da yau a kasar Libya?

Sai dai kisansa ya gaza taimaka wa wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya a kasar.

A cikin makon nan ne marigayi Shugaban Libya, Kanar Mu’ammar Ghaddafi ya cika shekara 10 da rasuwa, bayan da sojojin da suka yi tawaye suka kashe shi da sunan juyin juya-halin da ya jefa kasar a cikin rikici.

Rikicin na Libya da ya samu goyon bayan manyan kasashen duniya da Kungiyar Tsaro ta NATO, masana suna ganin shi ya assasa tashe-tashen hankali da bazuwar makamai a Nahiyar Afirka.

Marigyai Shugaba Mu’ammar Ghadhafi wanda ya mulki Libya na tsawon shekara 42 daga 1969 bayan karbe mulki daga hannun sarakuna da kasar ke bi a baya ya rasu ne a shekarar 2011 lokacin da kasashen duniya a karkashin jagorancin kasar Amurka suka yi wa gwamnatinsa taron dangi.

Sai dai kisansa ya gaza taimaka wa wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya, wanda da shi ne aka ta farfaganda wajen samun goyon bayan mutanen kasar don hambarar da mulkin nasa.

Shekara daya da kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin bangarorin da suke rikici da juna a kasar Libya amma masana suna ganin abu ne mai wuya zaben da ake shirin gudanarwa ya iya warware rikicin da Libya ke ciki.

A ranar 20 ga Oktoban shekarar 2011 ne wadansu ’yan tawaye suka bi marigay Shugaba Ghaddafi har zuwa mahaifarsa garin Sirte suka kashe shi a tsakiyar titi sannan suka ja gawarsa a tsakiyar kasuwa.

Har zuwa yau Libya ta gaza murmurewa daga illar da hambarar da gwamnatin Ghaddafi ta haifar mata, a bangaren zaman lafiya da tattalin arziki, sannan kasar ta hadu da kunci rayuwa sabanin sassaukar rayuwa da kasar ke yi a baya a zamanin marigayin.

Wani masani a cibiyar bincike ta Berisk Maplecroft, Hamis Kinnear ya ce kasar Libya ta fi kasancewa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a lokacin mulkin Ghaddafi, idan aka kwatanta da halin da take ciki a yanzu.

Bayan hambarar da Ghaddafi, matsalolin ’yan bindiga da masu safarar mutane suna bautar da su da kwararar baki zuwa Turai ta kasar baya ga barayin man fetur suka ta’azzara a kasar ta Arewacin Afirka.