✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Talatin da Bakwai:  Fifikon ciyarwa domin daukaka kalmar Allah: 530. An karbo daga Sa’id dan Hafsu ya ce: “Shaiban ya ba mu labari…

Babi na Talatin da Bakwai: 

Fifikon ciyarwa domin daukaka kalmar Allah:

530. An karbo daga Sa’id dan Hafsu ya ce: “Shaiban ya ba mu labari daga Yahya daga Abu Salma cewa: “Lallai shi ya ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya ciyar da abubuwa biyu domin daukaka kalmar Allah. Mai tsaron Aljanna zai rika kiransa ta kowace kofa, yana cewa: Taho nan! Taho nan! Sai Abubakar ya ce: “Ya Manzon Allah! Wannan mutum babu abin da  ke halaka shi.” Sai (Annabi) ya ce: “Ina kaunar ka kasance daga cikin wadanda za a kira daga wadannan kofofi.”

531. An karbo daga Muhammad dan Sinan ya ce: “Fulaihu ya ba mu labari ya ce, Hilal ya ba mu labari daga Adda’u dan Yassar daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya mike bisa mumbari sai ya ce: “Lallai abin da nake jin muku tsoro a bayana shi ne idan aka bude muku albakar kasa (dukiya mai yawa). Sa’an nan ya ambaci abin da ya shafi kawar (adon) duniya. Sai ya fara ambato na farko mai alheri bai ambaci na biyun ba.” Sai wani mutum ya mike ya ce: “Ya Manzon Allah! Shin alheri yana zuwa da sharri ne? Sai Annabi (SAW) ya yi shiru, muka ce: “Lallai za a yi masa wahayi, mutane suka yi shiru kamar ka ce, kawunansu akwai tsuntsaye. Sa’an nan ya shafe zufar (gumin) da ke bisa fuskarsa, sai ya ce: “Ina mai tambayar nan dazu? Ya ce: “Shin kana tsammani dukiya alheri ce? Ya maimaita haka kamar sau uku, tare da cewa: “Alheri ba ya haifar da komai face alheri. Hakika duk Abin da  gabar teku ta tsirar ko da ya yi kisa ne ko ya ce, ya yi kusa ga kisar dabbobin da ke kiwatawa saboda handama (zari) face makiyayar dabbobi wadda suke ci mai manya ganyaye cikakku (mai kosarwa). Sa’an nan idan suka tsayu ga rana su yi kashi da fitsari. Sai su ci gaba da kiwatawa. Wannan abin duniya (dukiya) kamar ’ya’yan itace ne mai zaki. Kuma madalla Musulmin kirki ya zamo mai ita, wanda zai rike bisa hakkinta, ya ciyar da ita domin daukaka kalmar Allah. Wanda bai rike bisa hakkinta ba, shi zai kasance kamar mai ci bai koshi. Kuma ya zamo masa mai shaida a kansa Ranar kiyama.”

Babi na Talatin da Takwas:

 Fifikon wanda ya shirya fita yaki ko ya rika lura da wasu mayakansa bisa alheri:

532. An karbo daga Abu Ma’amar ya ce: “Abdulwaris ya ba mu labari ya ce, Husain ya ba mu labari ya ce, Yahya ya ba ni labari ya ce, Abu Salma ya ba ni labari ya ce, Bishiru dan Sa’id ya ba ni labari ya ce: “Zaid dan Khalid (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya shirya wa fita yaki domin daukaka kalmar Allah, to, hakika ya yi yakin. Wanda kuma ya kyautata ga mayaka da alheri domin su daukaka kalmar Allah, hakika shi ma ya yi yakin.”

533. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Hamman ya ba mu labari daga Is’hak dan Abdullahi daga Anas (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya kasance bai shiga wani gida sosai a garin Madina da kamar yadda ke shiga gidan Ummi Sulaim. Sai dai gidansa ya fi shiga iyalansa. Da aka tambaye shi, sai ya ce: “Lallai ni, ina jinkanta ne, saboda an kashe dan uwanta da ke tare da ni a wajen yaki.”