Babban Limamin Masallacin Haramin Makkah, Sheikh Abdul Rahman Sudais ya yi Allah-wadai da masu aibata Annabi Muhammad (SAW).
A hudubarsa ta Juma’a a masallacin, Sheikh Sudais, wanda shi ne Ministan Masallatai Masu Alfarma na kasar Saudiyya ya nuna fushinsa tare da kausasa harshe a kan masu batanci ga Ma’aiki.
- Ganduje ne jagoran yaki da cin hanci a Najeriya —Salihu Tanko Yakasai
- #EndSARS: Filato ta yi asarar N75bn a kwana biyu
- Satar #EndSARS: Dalilin adanar kayan abincin gwamnati
Sudais ya bayyana masu irin wannan aiki a matsayin mutane marasa daraja da kima.
Tunda farko, limamin Haramin ya zayyano kyawawan halaye da dabi’un Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasallam, yana mai bayyana shi da amintacce, karimi, mai saukin hali wanda duniya ta cika da sanin daraja da matsayinsa.
A karshen hudubar, limamin ya ja kunnen masu afka wa janibin Manzon Allah da su kiyaye, su guji fushin Ubangiji da fitinar da za ta iya afka musu ko azaba mai radadi.
Sheikh Sudais ya rufe da addu’o’in neman zaman lafiya a kasashen Musulmi da duniya baki daya.
Hudubar ta Sheikh Sudais na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar Musulmi a duniya ke la’antar masu yin batanci ga Manzon Allah (SAW).
Dubun dubatar Musulmai sun yi ta kare martabar Ma’aiki (SAW) tare da kira da a kaurace wa kayan da aka kera a kasar Faransa, suna kuma yin tir da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Macron ya fara shan la’anta daga Musulmi a fadin duniya ne kan yadda ya goyi bayan masu batanci ga Ma’aiki a kasarsa bisa hujjar ‘yancin bayyana ra’ayi.
Baya ga Sheikh Sudai, manyan shugabannin kasashen Musulmi, kamar Shugaba Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan sun bukaci a yi wa Macron gwajin kwakwalwa saboda kalaman nasa da ya yi.
Ana iya tunawa tun a wuraren shekarar 2006 mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa ta wallafa zanen barkwancin Manzon Allah (SAW) wanda ya ja mata suka daga al’ummar Musulmi a fadin duniya.
Sai dai duk da wasu matakai da aka dauka kan kamfanin, ciki har da hari da aka sha kai wa ofishinsa inda aka hallaka wasu ma’aikatanta, da alamar ba su daddara ba.
Daga baya ma mujallar ta sake wallafa ire-iren hotunan, wanda ya sake ja mata suka da la’anta.