✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sheikh Jingir ya shawarci mutanen kirki su shiga siyasa

Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’ah wa Ikamatussunnah, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya shawarci mutanen kirki da su shiga cikin harkokin siyasa…

Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’ah wa Ikamatussunnah, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya shawarci mutanen kirki da su shiga cikin harkokin siyasa domin samun shugabanni nagari.

Sheikh Sani ya yi wannan kalami ne a wajen ganawarsa da manema labarai lokacin rufe wani babban taron wa’azin kasa da kungiyar ta gudanar a fadar Mai Martaba Sarkin Misau a Jihar Bauchi. Ya ce “siyasa na daga cikin tsarin musulunci, don haka ne na ke kira ga kowane musulmi da ya rungumi yin siyasa domin zabin shugabani nagari.”

Malamin ya ce sun shirya taron wa’azin kasan ne domin koyar da jama’ar musulmi sunnar Annabi da koyarwar Musulunci, kuma an samu nasarori da yawa a wannan wa’azin da aka yi a Misau.

Sheikh Jingir ya ce kungiyar Izala dai ta dukufa ne wajen koyarwar addinin Islama tsantsa, suna kuma gina makarantu a dukkanin matakai domin koyarwar da ilimi, suna gudanar da ayyukan jinkan jama’a da na agajin gaggawa domin kyautata rayuwar jama’ar kasa.

Da ya juya bayanin zaben 2019 da ke tafe kuwa, babban Malamin Izalar, ya  ce “siyasa tana daga cikin tsarin musulunci, kuma siyasa aba ce mai muhimmanci domin sai da ita rayuwa take inganta. Muna jan hankalin mutane su yi siyasa su yi jagoranci domin tsarin musulunci ne, Annabi (S) shi ne ya ce ‘Banu Isra’ila tun ma lokacin farko, ma su siyasarsu Annabawa ne. Sanda wani Annabin kwanansa ya kare ya wuce, sai wani ya maye. Don haka muna koyar da jama’a su sani siyasa addini ce, sai ta tsayu sallah zai yi kyau, don sai da siyasa za a kafa makarantu, sai siyasa ta tsayu za a samu karatu, in ba siyasa karatun ma zai yi rauni. Sai siyasa ta tsayu za a yi masana’antu, in ba siyasa za a zauna zaman banza, muna yaki da cima-zaune, muna yaki da tumasanci, muna yaki da damfara, ha’inci, muna kuma karfafar gwamnatoci kowa ya yi gaskiya a cikin hidimarsa ta rayuwa,” inji Shaihin malamin.

A jawabinsa, Mai Martaba Sarkin Misau, Alhaji Ahmad Suleiman ya jinjina wa kungiyar Izala a bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban Addinin Musulunci a Nijeriya. “Wannan kungiyar ta sa ilimi a gaba, don haka, mu za mu baiwa kungiyar Izala fili domin ta gina makaranta a wannan garin.”

Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Bauchi, Shaikh Salisu Sulaiman Ningi, ya nuna godiyarsu a bisa gudunmawar da gwamnatin Jihar Bauchi da Sarkin Misau suka basu wajen samun nasarar wannan taron.

Dangane da batun gina makaranta da Sarkin ya bijiro da ita kuwa,  Sheikh Salisu ya ce tuni shugaban majalisar Malamai na Izala ya amince kuma ya umurce su da duba yiwuwar hakan, kuma ya ce za su gina wannan makarantar kwanan nan.